Amarya Ta Kashe Ango a 'Wani Yanayi' bayan Kwana 3 da Daura Masu Aure a Katsina
- Mutanen yankin karamar hukumar Jibia a jihar Katsina sun ga tashin hankali bayan mutuwar sabon ango a kauyen Tashar Aibo
- Rahoto ya nuna cewa ana zargin amarya, Aisha ta yi amfani da wuka wajen hallaka mijinta, wanda sanannen dan kasuwa ne a yankin
- Mazauna yankin da ke iyaka da Nijar sun tabbatar da faruwar lamarin ga Legit Hausa, suka bayyana marigayin da mutumin kirki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Mutane sun shiga yanayin tashin hankali bayan wata amaryar kwanaki uku kacal ta hallaka mijinta a jihar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a kauyen Tashar Aibo da ke yankin karamar hukumar Jibia a jihar Katsina ranar Lahadi.

Source: Original
Tribune Nigeria ta tattaro cewa ana zargin amaryar mai suna Aisha Muhammad, ta daba wa angonta, Abubakar Dan Gaske, shahararren mai saida masara, wuka a wuya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin amarya ta kashe angonta
Mazauna yankin sun bayyana cewa su na zargin matar ta aikata wannan danyen aiki ne da yammacin jiya Lahadi, lokacin da mijin ya kwanta barci domin hutawa a gida.
An daura auren Dan Daske da amaryarsa ne a ranar Alhamis, 18 ga Nuwamba, 2025, kafin wannan mummunan al’amari ya faru kwana uku da fara angonci.
Shaidu sun ce matar ta yi amfani da wuka, ta soka wa mijinta a wuya a yayin da yake tsakiyar barci, wanda hakan ya yi sandiyyar mutuwarsa.
Mazauna yankin sun bayyana marigayin a matsayin mutum mai kirki, mai aiki tukuru kuma ya kasance wanda mutane ke kauna a kauyen saboda halinsa na kirki.
Leadership ta tattaro cewa mutane da dama sun taru a kusa da shagonsa a ranar Lahadi, cikin kaduwa da bakin ciki saboda wannan mugun labari.
Yadda lamarin ya faru a Katsina
Wata mai suna Lauratu Haruna, 'yar yankin da lamarin ya faru ta tabbatar wa Legit Hausa cewa ba auren dole aka yi wa Aisha ba, hasali ma tana son Dan Gaske.
A cewarta, wannan shi ne aurenta na biyu, kuma ana zargin ta kashe mijin ne bayan ta kira shi ya dawo gida ya ci abinci.
"Kwana uku da auren Aisha Muhammad da Abubakar Dan Gaske, ta yi ajalin mijinta har lahira bayan ta masa yankan rago. Mun yini da labari mai munin gaske, wanda muke jinsa a nesa damu a yau gashi a garinmu.
"Allah ka ji kansa da rahama, sannan muna kira da roko ga masu ruwa da tsaki da masu kare hakkin dan Adam, dan Allah su bi wannan abu domin tabbatar da adalci, domin a hukunta mai laifi.
Allah Ya sa mu dace, Allah Ka hana mu aikin da na sani," in ji ta.

Source: Facebook
Miji ya kashe matarsa a Sakkwato
A wani labarin, kun ji cewa wani matashi dan shekara 25 a duniya, Sufiyanu Aliyu ya halaka matarsa da wuka yayin da sabani ya shiga tsakaninsu a jihar Sakkwato.
Rahotanni sun nuna cewa rigima ta shiga tsakanin Sufiyanu da Suwaiba matarsa, daga bisani rigimar ta rikide zuwa fada mai zafi.
Rundunar 'yan sanda ta kama wanda ake zargin kuma tun kafin a je ko ina, ya amsa laifin kisan kan da ake masa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


