Sheikh Gumi Ya Fadi Matsalar da Ake Fuskanta wajen Kawar da Rashin Tsaro

Sheikh Gumi Ya Fadi Matsalar da Ake Fuskanta wajen Kawar da Rashin Tsaro

  • Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya sake yin tsokaci kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Najeriya
  • Sanannen malamin Musuluncin ya bukaci 'yan Najeriya da su kasance maau hakuri da juriya kan matsalolin rashin tsaron da ake fuskanta
  • Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa ko kasashen da suka ci gaba ba su tsira ba daga fuskantar matsalar rashin tsaro

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya roki ’yan Najeriya da su kasance masu hakuri su kuma guji fadawa cikin damuwa, duk da matsalolin tsaro da ake yawan fuskanta a kasar.

Sheikh Ahmad Gumi ya jaddada cewa babu wata gwamnati a duniya da za ta iya kawar da ta’addanci gaba ɗaya.

Sheikh Gumi ya yi magana kan rashin tsaro
Sanannen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi wadda ya sanya a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya sanya ranar fara azumi, addu'o'i, ya shawarci Musulmi, Kirista

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake mayar da martani kan sace-sacen mutane da ya faru kwanan nan a jihar Kwara da wasu sassan kasar, Gumi ya ce bai yiwuwa a yi tsammanin kawar da matsalar tsaro 100 bisa 100 ba.

Me Gumi ya ce kan rashin tsaro?

Malamin addinin Musuluncin ya ce har kasashe masu ci gaba na fama da kalubalen rashin tsaro.

“Babu wata gwamnati da za ta iya kawar da ta’addanci gaba ɗaya. Ko Amurka suna fama da matsalolin tsaro nasu.”

- Sheikh Ahmad Gumi

Ko da yake mutane na nuna kokawa kan yawan hare-hare da garkuwa da mutane, malamin ya ce lamuran tsaro na ingantawa sannu a hankali.

Ya yi kira ga ’yan kasa da su fahimci cigaban da ake samu maimakon mayar da hankali ga matsalolin da ke ci gaba da faruwa.

“Abubuwa suna ingantuwa. ’Yan Najeriya su yi hakuri su guji firgita.”

- Sheikh Ahmad Gumi

Kara karanta wannan

Sace dalibai: An taso Tinubu a gaba, malami ya buƙace shi don Allah ya yi murabus

Gumi ya jefi 'yan kasar waje da zargi

Gumi ya kuma yi gargadi kan cewa 'yan kasashen waje na kokarin amfani da addini domin kawo rarrabuwar kai a tsakanin ’yan Najeriya, musamman ta hanyar amfani da Kiristanci domin haifar da rashin amana tsakanin al’ummomi.

“Wasu mutane daga waje na kokarin yin amfani da Kiristanci domin raba kan ’yan Najeriya. Kada mu yarda da haka. Al’ummomin addini a Najeriya sun daɗe suna rayuwa tare cikin zaman lafiya.”

- Sheikh Ahmad Gumi

Sheikh Gumi ya yi tsokaci kan matsalar tsaro
Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Jawabinsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga da ta’addanci a fadin kasa.

Lamarin da ya sake tayar da tattaunawa kan alhakin gwamnati, tsaron ƙasa, da kuma tasirin aikin da ake yi na yaƙi da ta’addanci.

Gumi ya ragargaji masu son a kama shi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi martani mai zafi kan mutanen da ke neman a cafke shi saboda jagorantar sulhun da yake yi da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Bulama Bukarti ya fadi hanyoyi 5 da Tinubu zai bi ya kawo karshen rashin tsaro

Sheikh Gumi ya yi Allah wadai da irin kiran da wasu ke yi na a kama shi saboda tsokacin da yake yi kan batun ‘yan bindiga da tsaron kasa.

Malamin addinin Musuluncin ya bayyana masu son a kama shi a matsayin marasa tarbiyya da ke son hayaniya da tada kura fiye da fuskantar gaskiya kan matsalar tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng