Najeriya Ta Yi Rashi: Tsohon Gwamnan Bauchi, Babban Sarki, Abu Ali Ya Rasu
- Gwamnan Bauchi Bala A. Mohammed ya bayyana rasuwar Janar Abu Ali, yana kiran shi gwarzo kuma jajirtacce
- Marigayin ya jagoranci Bauchi daga Satumba 1990 zuwa Janairu 1992, inda ya aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa
- Bayan barin gidan soja, ya ci gaba da hidima a matsayin Sarkin Bassa Nge, inda ya samu girmamawa a faɗin Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayyana cewa ta shiga cikin jimami da alhini sakamakon rasuwar tsohon gwamnan soja na jihar, Birgediya Janar Abu Ali (Mai ritaya).
Janar Abu Ali ya shugabanci Bauchi tsakanin Satumba 1990 zuwa Janairu 1992 a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida, inda ya gudanar da ayyuka na ci gaban al’umma da suka bar tarihi.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamna Bala Mohammed ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayin da daukacin al’ummar jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bala Mohammed ya bayyana marigayin a matsayin shugaba mai hangen nesa da tsantseni wajen gudanar da al’amura.
Ayyukan Abu Ali a jihar Bauchi
A lokacin da ya ke kan mulki, Janar Abu Ali ya kaddamar da aikin ruwan Bauchi, wanda ya inganta samar da ruwa a babban birnin jihar.
Haka kuma ya taka rawar gani wajen karfafa kamfanin tumatur, abin da ya taimaka wajen bunkasa aikin gona da karin darajar amfanin gona.
Bugu da kari, shi ne ya kafa kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourists, wadda ta zama abin alfahari ga jihar.
Matakan da ya dauka a Tafawa Balewa
A shekarar 1991, lokacin da aka samu rikici a Tafawa Balewa da wasu yankuna, marigayin ya dauki matakai cikin gaggawa, inda ya kafa dokar hana fita tare da tura jami’an tsaro.
Wannan tsari ya taimaka wajen kwantar da tarzoma da hana ta rikidewa zuwa babban rikici, inda gwamna Bala Mohammed ya ce wannan lamari ya nuna kaifin basira da kishin kasa.
Abu Ali ya zama sarki bayan barin soja
Bayan saukarsa daga mulki a Janairun 1992, Janar Abu Ali ya mika mulki cikin lumana ga gwamnatin dimokuradiyya, abin da gwamna Bala ya kira “alamar biyayya ga kundin tsarin mulki.”
A shekarar 2000 kuma, marigayin ya zama Etsu Bassa Nge, sarautar gargajiya mai daraja ta farko a Jihar Kogi.
Ta'aziyyar gwamnan Bauchi, Bala Mohammed
Gwamna Bala Mohammed ya yi kira ga al’ummar Bauchi da su sanya iyalan marigayin cikin addu’o’i.

Source: Facebook
Ya ce Janar Abu Ali ya bar tarihi na shugabanci, karimci da kishin kasa wanda za a ci gaba da tunawa da shi.
Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai gaskiya, tawali’u da jajircewa ga al’ummarsa da kasa baki daya.
An kashe dan agajin Izala a Bauchi
A wani labarin, Legit Hausa ta kawo muku cewa wasu 'yan bindiga sun kashe wani dan agajin Izala a jihar Bauchi.
Bayanan da muka samu sun tabbatar da cewa an sace matar marigayin da 'yarsa karama da ake shayarwa yayin harin.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ke kokarin shawo kan matsalar tsaro da ta addabi kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


