Ba a Gama da Jihohin Kebbi da Neja ba, an Sace Mata a Jihar Borno
- Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta tabbatar da sace mata a yankin Mussa na Askira-Uba suna dawowa daga gona
- Kakakin 'yan sanda na jihar Nahum Daso ya ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga menama labarai a ranar Lahadi
- Al’ummar yankin sun nuna damuwa, musamman ganin yadda ake ta yawan sace-sace a jihohi daban-daban ƙasar nan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Wasu mata 12 sun afka hannun waɗanda ake zargin ’yan Boko Haram ne yayin da suke dawowa daga gonakinsu a ranar Asabar da yamma.
Al’amarin ya tayar da hankula a yankin, inda ake ci gaba da neman karin bayani kan yadda lamarin ya faru.

Source: Twitter
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da sace matan a sakon da ta wallafa a X, tare da bayyana cewa tana kan bincike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun yawaitar hare-haren satar mutane a wasu sassan ƙasar, lamarin da ya sanya jama’a cikin fargaba da kira ga gwamnati da jami’an tsaro.
An tabbatar da sace mata a Borno
Jami'in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Borno, Nahum Daso, ya ce an samu rahoton sace mata 12 a yankin Askira-Uba a ranar Asabar bayan dawowarsu daga gona.
Ya tabbatar da haka a tattaunawa ta waya da Punch a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa rundunar ta fara bincike.
Daso ya ce:
“An yi garkuwa a jiya a Askira-Uba. An sace mata 12 da ake zargin ‘yan Boko Haram sun yi musu kwanton bauna yayin da suke koma wa daga gona.”
Kakakin 'yan sandan ya ƙara da cewa al’amuran da ke tattare da lamarin har yanzu ba su gama bayyana ba.

Source: Facebook
Sai dai ya ce jami’an tsaro na cigaba da aiki domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma matakin da ya dace a ɗauka.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da hare hare, ƴan sanda sun yi karin haske kan zargin hari a cocin Gombe
Nahum Daso ya kuma yi kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu yayin da binciken 'yan sanda ke ci gaba.
Halin da aka shiga bayan sace mata
Wasu mazauna yankin sun bayyana damuwa kan yadda aka samu labarin sace matan da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, lokacin da ’yan uwansu suka kasa tantance inda matan suke.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun garzaya wajen shugabanninsu domin daukar matakin gaggawa.
A cewarsa:
“Labarin ya iso gare mu da ƙarfe 5:00 na yamma lokacin da ’yan uwansu suka kasa sanin inda suke. A matsayimu na al’umma, mun sanar da wakilanmu da shugabannin gargajiya har da hukumomin tsaro.”
An ba Tinubu bayani game da tsaro
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban hukumar DSS na kasa.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa an yi wa Bola Tinubu cikakken bayani ne game da halin da kasa ke ciki kan lamarin tsaro.
Hakan na zuwa ne bayan shugaba Tinubu ya fasa tafiye-tafiye saboda yawaitar sace mutane da kai hare-hare jihohi a kwanan nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
