Yan Bindiga Sun Harbe Dan Agajin Izalah, Sun Sace Matarsa da Jaririyar Mako 2

Yan Bindiga Sun Harbe Dan Agajin Izalah, Sun Sace Matarsa da Jaririyar Mako 2

  • Masu garkuwa da mutane sun kai hari a jihar Bauchi lamarin da ya ta da hankulan al'ummar yankin da aka kai farmaki
  • Maharan sun kashe mai hidima ga addini wanda ya kasance dan agajin kungiyar JIBWIS reshen Jos tare da sace iyalinsa
  • Shaidu sun ce maharan sun shiga kauyen da dare, suna harbe-harbe kafin su shiga gidansa, lamarin da ya jefa al’umma cikin tsoro da tashin hankali

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Toro, Bauchi - Ana zargin masu garkuwa da mutane da kai mummunan hari a wani kauye da ke jihar Bauchi a Arewa maso Gabas.

Maharan sun farmaki kauyen Zalau da ke cikin karamar hukumar Toro a jihar Bauchi da daren Asabar, 22 ga Nuwamba 2025.

Yan bindiga sun hallaka dan agajin Izalah a Bauchi
Kakakin rundunar yan sanda, CSP Mohammed Wakili. Hoto: Nigeria Police Force, Bauchi State Command.
Source: UGC

Bauchi: Yan bindiga sun hallaka dan agaji

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

Rahoton Tribune ya bayyana cewa a yayin harin, sun kashe wani dan agajin kungiyar Izalah reshen Jos, Alhaji Muhammad Bakoshi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce ba a tabbatar da adadin maharan ba, amma sun kai hari kai tsaye gidan marigayin, wanda shi ne jami’in ladabtarwa na kungiyar JIBWIS, reshen Zalau.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa bayan kashe dan agajin, an yi garkuwa da matarsa wacce ta haihu makonni biyu da suka gabata da kuma ‘yarsu mai shekaru biyar.

Shaidu sun fadi yadda abin ya faru

Wani mazaunin kauyen ya shaida cewa maharan sun shigo kauyen tsakanin ƙarfe 11:00 na dare zuwa 12:00 na dare, suna harbe-harbe sararin samaniya kafin su nufi gidansa kai tsaye.

Ya bayyana cewa lamarin ya jefa al’ummar garin cikin tsananin tsoro da damuwa, inda suka ce suna kara kasancewa cikin hadari saboda yawan hare-haren ‘yan bindiga a yankin.

Wasu yan bindiga sun hallaka dan agajin Izalah
Taswirar jihar Bauchi da wasu lokuta ake kai harin yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Halin da ake ciki bayan harin yan bindiga

Majiyar ta kara cewa al’umma na ta addu’a domin a dawo da wadanda aka sace lafiya, tare da karfin gwiwa ga iyalan da suka rasa masoyinsu a wannan mawuyacin hali, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Cocin katolika ya fadi halin da ake ciki bayan sace dalibai a Neja

Mazaunin ya kuma ce:

"Yan bindiga da masu garkuwa a Najeriya ba sa bibiyar addini. Suna kai hari ga duk wanda suka ga dama, ya kamata mu mayar da hankali kan tsaro da hadin kai ba rarrabuwa ba.”

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ba ta mayar da martani kan lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Kakakin rundunar yan sanda a Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil, bai amsa sakon WhatsApp da wakilin Legit Hausa ya tura masa ba.

Yan bindiga farmaki yan sanda a Bauchi

Mun ba ku labarin cewa 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun shammaci jami'an 'yan sanda bayan da suka fita aikin sintiri a jihar Bauchi.

Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka wasu daga cikin jami'an 'yan sandan da suka kai wa hari lokacin da suka fita kare rayukan 'yan Najeriya da dukiyoyinsu.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa harin ba zai sanya gwiwoyin jami'anta su yi sanyi ba wajen tabbatar da tsaro da kare rayukan al'umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.