Ana tsaka da Hare Hare, Ƴan Sanda Sun Yi Karin Haske kan Zargin Hari a Cocin Gombe

Ana tsaka da Hare Hare, Ƴan Sanda Sun Yi Karin Haske kan Zargin Hari a Cocin Gombe

  • Rundunar ‘yan sanda ta Gombe ta yi karin haske game da jita-jitar da ake yadawa game da hari a coci
  • Rundunar ta karyata rahoton harin coci da sace mutane da ya yadu a kafofin sadarwa tana shawartar al'umma
  • Rahoton ya zo ne a lokacin da Najeriya ke fama da jerin hare-haren sace ɗalibai da masu ibada da sauran al'umma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Rundunar yan sanda a jihar Gombe ta yi magana kan rade-radin da ake yadawa kan farmaki a wani coci.

Rundunar ta musanta labarin inda ta ce kwata-kwata babu kamshin gaskiya kan abin da ake yadawa.

Yan sanda sun karyata kai hari kan coci
Kakakin yan sanda a Gombe. Hoto: Buharee Abdullahi Dam Roni.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da kakakin yan sanda, Buharee Abdullahi Dam Roni ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yaɗa jita-jitar kai hari a cocin Gombe

Kara karanta wannan

An yi yunkurin kashe alkalin da ya yanke wa Nnamdi Kanu hukunci? Kotu ta yi bayani

Sanarwar ta ƙaryata rahotannin da ke yawo cewa ‘yan bindiga sun kai hari cocin ECWA tare da sace mambobi, tana cewa bayanin karya ne.

An ce wata mai suna Shallangwa, ta wallafa labarin a Facebook wanda Legit Hausa ta bincika da ya nuna alamun ta goge rubutun da ta yi.

A cikin rubutunta, ta ce:

“Na fito daga coci kawai sai na samu kiran waya daga wata kawata ta a Gombe.
“Suna ibada a wani cocin ECWA a Gombe. An yi garkuwa da mambobin cocin. Ba da dadewa ba, a bainar jama’a….”
An musanta kai hari a cocin Gombe
Taswirar jihar Gombe da ke Arewa maso Gabas a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yan sanda sun musanta kai hari Gombe

Buhari ya bayyana cewa babu wani hari da ya faru a cocin, ya kuma gargadi jama’a su daina yada rahotannin da ba a tantance ba a kafafen sada zumunta.

A cewar sanarwar:

“Cocin ECWA da ake magana akai, Babban Jami’in ‘Yan Sanda (CSP) da Sufeton ‘Yan Sanda (SP) da wasu jami’ai suna can tun ƙarfe 6:00 na safe, kuma babu abin da yake faruwa a wurin. Don haka wannan labari ƙarya ne kuma ya saɓa wa gaskiya.”

Kara karanta wannan

Ana neman daliban Kebbi, 'yan sanda sun ceto mata 25 da aka yi garkuwa da su

Yadda ake fama da hare-haren yan bindiga

Har yanzu Najeriya na fama da sace mutane da dama, ciki har da ɗaliban Chibok na 2014, lamarin da ya sa duniya ke cigaba da nuna damuwa.

A kwanakin baya, an sace ɗalibai 303 da malamai 12 a makarantar St. Mary a jihar Niger, sannan aka sake sace wasu ‘yan mata 25 a Kebbi.

A Kwara, ‘yan bindiga kusan 10 sun kai hari cocin CAC inda suka bindige mambobi, suka kuma tafi da masu ibada 38 tare da kashe fasto.

Legit Hausa ta tattauna da dan Gombe

Muhammad Sani Yahaya ya bayyana damuwa game da yada jita-jitar musamman game da kawo rabuwar kai a addini.

Ya ce:

"Yan bindiga da masu garkuwa a Najeriya ba sa bambance kowane addini, suna farmakin jama'a ne kowanda suka ga dama, ya kamata mu mayar da hankali kan tsaro da hadin kai ba rarrabuwa ba.”

Ya shawarci al'umma su guji yada jita-jita saboda yana kawo tsaiko musamman yadda ake kokarin samar da tsaro a Gombe.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa har yanzu ba a hukunta 'masu' daukar nauyin ta'addanci ba': Minista

An sace dalibai da malamai a Niger

Mun ba ku labarin cewa rahotanni sun ce an sace dalibai da ma’aikata da ba a tantance adadinsu ba a makarantar St. Mary’s da ke Niger.

An ce ’yan ta’adda sun kutsa makarantar ne da misalin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na dare, ana ci gaba da tantance abin da ya faru.

Lamarin ya biyo bayan sace dalibai a wata makarantar mata a Kebbi da rufe makarantu da dama a Kwara cikin mako guda.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.