Ta Kacame Tsakanin Gwamnatin Kebbi da Sanata kan Matsalar Tsaro

Ta Kacame Tsakanin Gwamnatin Kebbi da Sanata kan Matsalar Tsaro

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta kasa kawar da kai kan wasu kalamai da Sanata Garba Maidoki ya yi dangane da batun tsaro
  • Ta bayyana cewa babu kamshin gaskiya a cikin kalaman nasa kuma ya yi su ne d. Nufin karkatar da gaskiya
  • Gwamnatin ta bayyana irin kokarin da take yi wajen samar da tsaro da kuma ayyukan ci gaba da take gudanarwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta yi kakkausar suka ga Sanata Garba Maidoki kan kalaman da ya yi dangane da tsaro da ayyukan cigaba a jihar.

Gwamnatin ta bayyana kalaman nasa a matsayin marasa tushe kuma kokarin karkatar da gaskiya.

Gwamnatin Kebbi ta yi wa Garba Maidoki martani
Sanata Garba Maidoki da Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris Hoto: Sen. Garba Musa Maidoki, Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Gwamna Nasir Idris shawara kan harkokin sadarwa, Abdullahi Idris ya fitar ranar Lahadi, 23 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Gwamnatin Kebbi ta dauki mataki kan makarantu bayan sace dalibai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me gwamnatin Kebbi ta ce kan Maidoki?

Gwamnatin ta ce kalaman Maidoki an yi su ne da nufin rage kimar kokarin ake yi wajen inganta tsaro, musamman bayan sace daliban makarantar GGCSS, Maga.

Sadaukin Zuru ya musanta ikirarin sanatan cewa an raba al’ummomi 200 da muhallansu saboda hare-haren ’yan bindiga, rahoton New Telegraph ya tabbatar da labarin.

"Bayanan gwamnati sun tabbatar cewa kimanin al’ummomi 50 ne daga yankin Wasagu–Sakaba suka fuskanci matsala, kuma an mayar da su gida cikin nasara ta hanyar haɗin gwiwar jami’an tsaro da aka tura bisa bukatar Gwamna Nasir Idris."

- Abdullahi Idris

Ya kara da cewa hedkwatar tsaro ce ke kula da tura dakarun sojoji da tsarin gudanar da ayyukan kai farmaki, inda ake sanar da gwamnan halin da ake ciki tare da samar da dukkan kayan aiki da ake buƙata.

Sanarwar ta kuma bayyana wasu muhimman matakan tsaro na gwamnatin, waɗanda suka haɗa da, samar da motocin Hilux sama da 100, rarraba babura 5,000 ga jami’an tsaro da shirya manyan tarukan tsaro da suka haɗa manyan malamai, sarakunan gargajiya da manyan hafsoshin tsaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi abin da tawagarta karkashin Ribadu ke yi a Amurka

Gwamnatin Kebbi ta caccaki Sanata Garba Maidoki
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, a wajen wani taro Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Game da ayyuka, gwamnatin ta ce ana ci gaba da aikin gyaran titin tarayya na Koko–Zuru da ya dade a lalace a karkashin gwamnatin Nasir Idris, kuma sanatan yana da cikakkiyar masaniya game da ci gaban aikin.

An zargi Maidoki da adawa da ayyukan gwamnati

Gwamnatin ta kuma zargi Maidoki da kasancewa cikin masu adawa da ayyuka masu amfani ga jama’a, tana mai cewa bai halarci ko daya daga cikin tarurrukan tsaro ko tattaunawar masu ruwa da tsaki da aka shirya domin wakilan yankunan da abin ya shafa ba.

Haka kuma, ta ce sanatan yana kokarin amfani da siyasa da nufin gurgunta gwamnatin APC a jihar.

“Ba mu yi mamaki da irin wannan matsayar ta sa ba, ganin cewa yana da alaka da ɗan takarar gwamna na ADC, Abubakar Malami.”

- Abdullahi Idris

Gwamnatin Kebbi ta rufe makarantu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta bada umarnin rufe makarantun sakandire a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Ta ya haka ta kasance: Gwamnatin Kebbi ta gano matsalar da ta auku kafin sace dalibai

Gwamnatin ta kuma umarci a kulle dukkanin manyan makarantu da ke fadin jihar, banda guda daya da ke cikin Birnin Kebbi.

Ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne sakamakon matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a wasu sassan jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng