Hotuna: Bayan Harin Kebbi, Neja, Iyaye Sun Kwashe Ƴaƴansu daga Makarantar Abuja

Hotuna: Bayan Harin Kebbi, Neja, Iyaye Sun Kwashe Ƴaƴansu daga Makarantar Abuja

  • Iyaye sun cika FGGC Bwari domin kwashe ’ya’yansu bayan umarnin rufe makarantu 47 sakamakon tsananin barazanar tsaro a yankunan Arewa
  • Matsalar fargabar tsaro ta karu bayan sace dalibai a Kebbi da Niger, lamarin da ya tilasta gwamnati gaggawar rufe makarantun Unity Colleges
  • FG ta ce rufe makarantun na wucin gadi ne domin kare rayuka, yayin da hare-haren ‘yan bindiga kan dalibai ke kara ta’azzara a jihohi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Cikin fargaba, iyaye sun fara kwashe ’ya’yansu daga makarantar FGGC Bwari da ke Abuja a ranar Asabar, bayan karuwar matsalar tsaro a yankin.

A gaban kofar makarantar an ga iyaye da ke dauke da jakunkuna, takardun makaranta da kayan kwana, wasu kuma na riƙe da ’ya’yansu cike da hawaye.

Iyaye sun kwashe 'ya'yansu daga FGGC Bwari bayan umarnin gwamnatin tarayya.
Dalibai mata na kokarin tafiya gida daga makarantar FGGC Bwari bayan umarnin gwamnati. Hoto: @channelstv
Source: Twitter

Dalibai na komawa gida bayan rufe makarantu

Kara karanta wannan

Mai Mala Buni: Gwamna ya hango hadari, ya rufe dukkan makarantun kwana

Hotunan da Channels TV ya wallafa a shafinsa na X ya nuna yadda wasu daruruwan dalibai suka rika shirya kayansu suna kokarin tafiya gida cikin gaggawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ga wasu dalibai sanye da kayan makaranta suna tattara kayansu, wasu kuma suna taimakon abokansu, yayin da motocin haya, na iyaye da manyan bas ke cunkushe a wajen, suna dibar daliban.

A ranar Juma’a, gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun FUC guda 47, ciki har da FGGC Bwari, saboda tsananin barazanar sace-sacen dalibai da ya kara ta’azzara a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Umarnin na kunshe ne a wata takarda da Daraktar Makarantun Sakandare (SSE), Hajiya Binta Abdulkadir, ta sanya wa hannu.

Barazanar tsaro na kara kamari a Najeriya

Najeriya ta fada cikin wani sabon yanayi na yawaitar sace dalibai cikin mako guda a yankunan Arewa.

A ranar 17 ga Nuwamba, ’yan bindiga suka kai hari makarantar kwana ta mata da ke Magana, jihar Kebbi, inda suka yi garkuwa da kusan dalibai 25, suka kashe mataimakin shugaban makarantar.

A ranar 21 ga Nuwamba, an sake kai hari makarantar firamare da sakandare ta St. Mary’s Catholic da ke a Papiri, karamar hukumar Agwara, jihar Niger. Har yanzu ba a bayyana adadin daliban da aka sace ba.

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

Wadannan hare-hare sun tayar da hankalin gwamnati, iyaye da al’umma baki daya, abin da ya sa gwamnati ta hanzarta rufe makarantu 47 domin kariya.

Hotunan sun nuna lokacin da iyaye ke taimakawa 'ya'yansu suna kwashe kayansu daga FGGC Bawari.
Hotunan sun nuna lokacin da iyaye ke taimakawa 'ya'yansu suna kwashe kayansu daga FGGC Bawari. Hoto: @channelstv
Source: Twitter

Wasu iyaye sun yi martani kan rufe makarantu

Wasu iyaye da Legit.ng Hausa ta ji ta bakin su sun bayyana damuwarsu game da yawaitar sace-sacen dalibai.

Malam Muhammadu Inuwa da ke zaune a Dan Mani, Rigasa, Kaduna, ya bayyana cewa:

"Tun jiya na je na dauko yaro na a nan GFC Kaduna, saboda tun kafin a fitar da sanarwar muke cike da zulumin halin da 'ya'yanmu suke ciki.
"Ka san dole labari zai rika yawo har a cikin makarantunsu, to ba za su samu natsuwa ba, za su rika tunanin ko su ma za a iya zuwa a sace su.
"Amma cikin ikon Allah, mun dawo da yaranmu gida, kuma muna rokon Allah ya kubutar da sauran yaran da aka sace. Wallahi dole kowane uba ya tausayawa iyayen da aka dauki 'ya'yansu."

Wani malami a makarantar FGGC Bakori, jihar Katsina, ya ce tun bayan sanarwar gwamnati suka hada kan dalibai, aka kuma fadawa iyayensu su zo su dauke su.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai

Malamin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce har zuwa yau Lahadi iyaye na kan zuwa daukar 'ya'yansu, musamman la'akari da cewa shiyyar Funtua ta na fama da nata matsalar tsaron.

"Mu dama mun dade muna fama da matsalar tsaro, kawai dai Allah na kare mu ne, ba a kawo mana hari cikin makaranta ba. Amma za ka ji ana shiga kauyukan da ke makotaka da mu, kamar su Sabuwar Abuja, Kurami da sauran garuruwa.
"Gaskiya gwamnati ta yi abin da ya dace da ta ba da umarnin rufe makarantu. Su kansu iyaye za su fi jin kwanciyar hankali idan 'ya'yansu suna tare da su."

Kalli hotunan FGGC Bwari a nan kasa:

An rufe makarantun kwana a jihar Yobe

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Yobe ta rufe dukkan makarantun kwana saboda barazanar tsaro, bayan hare-hare a wasu jihohin Arewa.

Sace dalibai da aka yi a makarantun jihohin Kebbi da Neja sun tilasta jihohi da dama daukar matakan kariya, ciki har da rufe makarantun gwamnati.

Gwamnatin Yobe karkashin Gwamna Mai Mala Buni ya jaddada cewa rufe makarantun ta ɗan lokaci ne, tare da rokon jama’a su dage da addu’a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com