Tsohon Minista: 'Abin da Ya Sa 'Yan Bindiga Ke Garkuwa da Yara 'Yan Makaranta'

Tsohon Minista: 'Abin da Ya Sa 'Yan Bindiga Ke Garkuwa da Yara 'Yan Makaranta'

  • Jerry Gana ya bayyana cewa barazanar shugaban Amurka ta sa 'yan bindiga suka fara yin garkuwa da yara 'yan makaranta
  • Tsohon ministan ya ce 'yan ta’adda na tserewa cikin dazuzzuka suna tattara fararen hula domin kare kansu daga hare-hare
  • Gana ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashen waje wajen kai wa 'yan bindiga farmaki ta sama

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon minista, Farfesa Jerry Gana, ya yi tsokaci kan yadda 'yan bindiga ke yawan sace dalibai a 'yan kwanakin nan.

Jerry Gana ya ce yawaitar sace-sacen dalibai a Arewacin Najeriya ka iya zama wani yunkuri na ‘yan bindiga na samu abin garkuwa daga barazanar Donald Trump.

Tsohon minista, Jerry Gana ya yi magana kan dalilin 'yan bindiga na sace 'yan makaranta.
Tsohon ministan labarai, Jerry Gana a lokacin da yake jawabi a wani taro. Hoto: @JerryGana
Source: Twitter

''Yan ta'adda na tsoron harin Trump' - Gana

A cewar tsohon ministan, 'yan ta'addar suna sace da cewa Trump ya yi barazanar kai hare-hare kan ƙungiyoyin ta’addanci a Najeriya, don haka suke shirin kare kansu., in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Ana jimamin sace dalibai, 'yan bindiga sun yi wa jami'an 'yan sanda kwanton bauna

Ya bayyana haka ne a Abuja yayin taron murnar samun matsayin shugaban majalisar hukumar kwastam ta Duniya da Kwanturolan kwastam na Najeriya Adewale Adeniyi ya sam.

Gana, wanda ya yaba da nadin Adeniyi a WCO, ya ce sace dalibai da ke faruwa a Kebbi da Niger wani shiryayyen al'amari ne.

Tsohon ministan ya ce 'yan ta'addar na tsoron cewa za a fara kai musu hari ta sama, don haka suka sace dalibai don su kare kansu.

Dalilin 'yan bindiga na sace yara dalibai

Farfesa Jerry Gana ya fadawa mahalarta taron cewa:

“Wani ya kira ni kafin na zo nan, ya fada mun cewa ‘yan bindiga sun ɗauki barazanar shugaban Amurka da muhimmanci. Saboda haka suke tattara yara domin su zama kariya a gare su.”

Ya ce tsarin yadda hare-haren ke faruwa na nuni da cewa ’yan bindigar na janyewa cikin dazuzzuka domin su nemi wurin ɓuya daga yiwuwar kai musu hari ta sama.

Kara karanta wannan

"Akwai wata a kasa": Sheikh Ahmad Gumi ya hango manufar sace dalibai

Jerry Gana ya ƙara da cewa:

“Sun san ana iya kai musu hari daga sama. Don haka suke kokarin samun fararen hula domin kare kansu.”

Gana ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa da Amurka da sauran abokan hulɗa domin kai farmaki ga sansanonin ’yan ta’adda cikin hikima, in ji rahoton The Guardian.

Sai dai jaridar Legit.ng Hausa ba ta iya tantance sahihancin ikirarin da Farfesa Jerry Gana ya yi ba.

Ministan Najeriya ya yi tsokaci kan tsaro

Ministan labarai, Mohammed Idris ya ce ana kokari wajen ceto daliban da aka sace.
Hoton ministan labaran Najeriya, Mohammed Idris a lokacin da yake jawabi a Abuja. Hoto: @HMMohammedIdris
Source: Twitter

A wurin taron, ministan labarai, Idris Mohammed ya ce kafafen yada labarai na ƙasashen waje na matsa masa lamba domin sanin ainihin adadin daliban da aka sace a Kebbi da Niger.

“Na samu sakonni daga kafafen waje suna tambayata adadin waɗanda aka sace a Agwara,” in ji Idris.

Ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na aiki tukuru don kubutar da daliban, tare da tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen magance matsalar tsaro ba.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Sojojin Najeriya sun hallaka kwamandan 'yan bindiga a jihar Neja

Sheikh Gumi ya hango manufar sace dalibai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, malamin Musulunci, Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi tsokaci kan karuwar sace-sacen dalibai a Najeriya.

Sheikh Ahmad Gumi ya nuna cewa akwai alaka tsakanin sace dalibai 'yan makaranta da zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi.

Fitaccen malamin Musuluncin ya yi fatan cewa da yardar Allah matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a kasar nan ta kusa zuwa karshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com