Ana Jimamin Sace Dalibai, 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an 'Yan Sanda Kwanton Bauna
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun shammaci jami'an 'yan sanda bayan da suka fita aikin sintiri a jihar Bauchi
- Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka wasu daga cikin jami'an 'yan sandan da suka kai wa hari lokacin da suka fita kare rayukan 'yan Najeriya
- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa harin ba zai sanya gwiwoyin jami'anta su yi sanyi ba wajen tabbatar da tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan jami'an ’yan sanda a jihar Bauchi.
'Yan bindigan sun hallaka 'yan sanda biyu bayan da suka kai musu farmaki yayin da suke gudanar da aikin sintiri.

Source: Facebook
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Najeriya, Benjamin Hundeyin, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda 'yan bindiga suka farmaki 'yan sanda
Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa tawagar ’yan sandan ta fita sintirin tabbatar da tsaro a Sabon Sara. Ya ce sun fita sintirin ne domin kara tabbatar wa mazauna yankin da cewa jami’an tsaro suna kan aiki, sai kuma kwatsam aka kai musu hari.
“Domin cika alkawarin kare ’yan Najeriya, haɗaɗɗiyar tawagar Rapid Response Squad (RRS), Police Mobile Force (PMF) da State Intelligence Department (SID) ta fita aikin sintiri a Sabon Sara, Bauchi."
"Abin takaici, an kai wa tawagar hari, lamarin da ya jawo mutuwar jami’anmu biyu da kuma raunata wani daban.”
- Benjamin Hundeyin
Benjamin Hundeyin ya ce an fara kokarin gano wadanda suka kai harin tare da tabbatarwa ’yan Najeriya cewa duk da rasa jami’ai a bakin aiki, rundunar ’yan sanda za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare rayukan jama’a.
“Muna bakin cikin rasa jami’anmu a yayin aikin da doka ta dora musu, amma ba za mu gaji ba wajen tabbatar da tsaron ’yan Najeriya baki ɗaya.”
- Benjamin Hundeyin

Source: Original
'Yan bindiga na kai hare-hare
Wannan sabon harin ya kara nuna yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a sassan Najeriya, inda kungiyoyin ’yan bindiga ke kashe jama’a da garkuwa da su ba tare da tsoro ko fargaba ba.
A ranar Juma'a, an yi garkuwa da dalibai sama da 300 a wata makarantar Katolika a jihar Neja, yayin da aka sace dalibai Musulmai 24 daga wata makaranta a jihar Kebbi.
A jihar Kwara, wasu ’yan bindiga sun kai hari a wani coci inda suka yi garkuwa da masu ibada da dama.
Duk da waɗannan hare-hare, babu wanda aka sako daga cikin waɗanda aka sace zuwa lokacin rubuta wannan rahoto.
Sojoji sun hallaka jagoran 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga a jihar Neja.
Jiragen yaki na sojojin sun samu nasarar hallaka daya daga cikin manyan jagororin 'yan bindiga da suka addabi al'umma a jihar Neja.

Kara karanta wannan
Bayan kashe Kiristoci a coci, ƴan bindiga sun sake kai hari Kwara, sun sace mutane
Ruwan wutar da sojojin suka yi ta jawo an hallaka Babangida, ɗaya daga cikin sanannun kwamandojin ’yan bindiga a karamar hukumar Shiroro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

