Mai Mala Buni: Gwamna Ya Hango Hadari, Ya Rufe Dukkan Makarantun Kwana

Mai Mala Buni: Gwamna Ya Hango Hadari, Ya Rufe Dukkan Makarantun Kwana

  • Gwamnatin Yobe ta rufe dukkan makarantun kwana saboda barazanar tsaro, bayan hare-hare a wasu jihohin Arewa
  • Matsalolin tsaro a Kebbi da Neja sun tilasta jihohi da dama daukar matakan kariya, ciki har da rufe makarantun gwamnati
  • Gwamna Mai Mala Buni ya jaddada cewa rufe makarantun ta ɗan lokaci ne, tare da rokon jama’a su dage da addu’a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ta umarci a rufe dukkan makarantun sakandare na kwana a faɗin jihar domin kare ɗalibai daga barazanar tsaro da ke ƙara tashi a wasu sassan ƙasar.

Wannan umarni ya fito ne daga bakin Mamman Mohammed, Darakta Janar na Yada Labarai ga Gwamna Mai Mala Buni, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Gwamna Mai Mala Buni ya ba da umarnin rufe dukkan makarantun kwana a Yobe.
Hoton gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a ofishinsa da ke Damaturu. Hoto: @HassanPeppe
Source: Twitter

An rufe makarantun kwana a Yobe

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Gwamnatin Kebbi ta dauki mataki kan makarantu bayan sace dalibai

Mohammed ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne bayan wani taron tsaro da gwamnan jihar ya yi tare da shugabannin jami’an tsaro, in ji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A taron, an yi nazari kan yadda ake samun faruwar hare-hare a makarantun wasu jihohin ƙasar. Wannan ya kai ga daukar matakin rufe makarantun sakandare na kwana har sai an samu ingantacciyar sauyi."

- Mamman Mohammed.

Sanarwar ta ce wasika daga Ma’aikatar Ilimi ta Sakandare, mai ɗauke da sa hannun Dr. Bukar Aji Bukar, ta umarci a rufe makarantun nan take.

Gwamna Buni ya roki al’ummar jihar su ci gaba da yin addu’a ga shugabanni, jami’an tsaro, da zaman lafiya a ƙasar baki ɗaya.

Rufe makarantu da matsalar tsaro a Arewa

Tun a ranar Asabar, Gwamna Agbu Kefas na Taraba ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kwana a jihar saboda fargabar harin ‘yan bindiga.

Ya ce dukkan ɗaliban kwana za su cigaba da zuwa makaranta a matsayin ɗaliban jeka-ka-dawo domin rage haɗarin tsaro.

Cikin kwanaki uku da suka wuce, an rufe makarantun jihohi da dama sakamakon karuwar hare-hare da garkuwa da ɗalibai.

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

A jihar Kebbi da Neja, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai fiye da 300 da malamansu, wanda ya jawo tashin hankali, in rahoton The Guardian.

Saboda wannan, gwamnatin tarayya ta rufe makarantu 41, yayin da sauran jihohi kamar Kwara, Neja, Filato, Katsina da Taraba suka sake duba tsarin gudanar da makarantu.

Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantu a sassan najeriya
hoton azuzuwan makarantar mata ta Dapchi da ke jihar Yobe. Getty Images
Source: Getty Images

An rufe makarantu a Filato

A jihar Plateau, hukumar PSUBEB ta ba da umarnin rufe dukkan makarantu bayan rahoton tsaro ya nuna cewa akwai makarantun firamare da sakandare da ake shirin kai wa hari.

Wannan na zuwa bayan da har yanzu dalibai mata 25 na makarantar GGCSS, Maga, jihar Kebbi suke hannun ‘yan bindiga bayan a sace su.

Hukumar PSUBEB ta ce rufe makarantun na ɗan lokaci ne, domin kare rayukan ɗalibai da tabbatar da cewa gwamnati na daukar tsaro a matsayin muhimmiyar al’amari.

Kwara; An rufe makarantu a garuruwa 4

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kwara ta bada umarnin rufe dukkanin makarantu kananan hukumomi hudu saboda karuwar tsaro.

Sanarwar da NUT ta karanta ta ce za a rufe makarantu a kananan hukumomi hudu ciki har da Irepodun, Ifelodun da Ekiti.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai

Gwamna AbdulRahman Abdulrazaq ya bukaci a kafa sansanin soji a yanin Eruku, garin da 'yan bindiga suka kai hari suka sace masu ibada.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com