Trump: Malaman Musulunci da Kirista Sun Hada Kai, Sun Shawarci Mabiyansu
- Malaman Musulunci da na Kiristanci sun yi magana game da barazanar Donald Trump na Amurka kan zargin kisan kiyashi
- Kungiyarsu ta IDFP ta gargadi ‘yan Najeriya su kwantar da hankali bayan kalaman Trump na cewa ana kisan Kirista da ya tayar da kura
- Shugabannin addinin sun ce kalaman na iya hura wutar rikici, suka roki kowa ya guji daukar fansa, da ba da muhimmanci ga tattaunawa da zaman lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugabannin Kirista da Musulmi sun bayyana matsayarsu game da kalaman Donald Trump kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.
Gamayyar malaman karkashin kungiyar IDFP sun nemi ‘yan Najeriya su kasance cikin natsuwa da hadin kai bayan kalaman Trump.

Source: Getty Images
A cikin sanarwar da shugabanninta suka sanyawa hannu, IDFP ta ce fargaba da tashin hankali ba za su kawo mafita ba, sai tattaunawa, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Trump ya sake fusata kan hare-haren miyagu
Shugaba Donald Trump ya kara fusata game da hare-haren da 'yan ta'adda ke kai wa kan fararen hula musamman Kiristoci a Najeriya.
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan farmakin da 'yan bindiga suka kai tare da sace dalibai da dama a jihohin Kebbi da Niger.
Trump ya bayyana Najeriya a matsayin abin kunya, tare da barazanar cewa Amurka za ta dakatar da tallafin da take ba kasar.
Wannan ya kara sanya tsoro a zukatan yan Najeriya duba da cewa har yau ana ta kokarin ganin an shawo kan lamarin amma bai samu ba.

Source: Facebook
Kungiya ta fadi illar maganganun Donald Trump
Kungiyar ta gargadi cewa maganganun Trump na iya tunzura masu mabambantan ra’ayi, don haka ya zama wajibi ka da a bari su tayar da rikicin addini.
Shugabannin sun ce kowa ya guji daukar fansa, ya kare kalamansa, ya kuma fifita zaman lafiya da fahimta a wannan lokaci mai matukar tsanani.

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka, Trump ya kara daukar zafi, ya kira Najeriya da kalma mara dadin ji
Kungiyar ta jaddada cewa matsalolin Najeriya za su warware ne idan an karfafa hadin kai, adalci da mutunta juna tsakanin mabambantan al’umma.
Bukatar malaman Musulmi, Kirista ga yan Najeriya
IDFP ta kuma bukaci gwamnati ta dauki matakan tabbatar da adalci da kare rayuka, domin babu ci gaba sai da gaskiya da daidaito ga kowa, The Guardian ta ruwaito.
Kungiyar mai wakiltar shugabannin addinai sama da 120 ta sha alwashin ci gaba da yaki da kalaman kiyayya da karfafa zumunci duba da halin da ake ciki yanzu.
Sun tunatar da jama’a cewa zaman lafiya yana bukatar kwantar da hankali, suna cewa “zabin hadin kai, tattaunawa da fata, domin haka ke kawo cigaba.”
An fadi abin da ya kai Ribadu Amurka
Kun ji cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta yi karin haske kan abin da ya kai tawagarta karkashin Nuhu Ribadu Amurka yayin da ake kallon kallo a tsakani.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana cewa tawagar gwamnati a Amurka na kokarin gyara labaran karya da ke zargin wariyar addini.

Kara karanta wannan
Faston da ya fara maganar kisan Kiristoci ya sake bayyana a gaban majalisar Amurka
Ya ce sun mika hujjoji ga hukumomin Amurka, suna bayani kan tsaro da yadda gwamnati ke kare ‘yan Najeriya ba tare da bambancin addini ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
