Iyalan Nnamdi Kano Sun ‘Gano' Makarkashiyar Hallaka Shi Bayan Tura Shi Sokoto

Iyalan Nnamdi Kano Sun ‘Gano' Makarkashiyar Hallaka Shi Bayan Tura Shi Sokoto

  • Iyalan shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu sun nuna damuwa kan makarkashiya da ake shiryawa dan uwansu
  • Dangin Kanu suka ce akwai makirci na hallaka shi bayan kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai kan tuhumar ta’addanci
  • Mutanen sun bukaci ƙasashen duniya su daura alhakin duk abin da ya faru da Kanu kan gwamnati da shugabanni a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Iyalan shugaban IPOB da aka haramta, Nnamdi Kanu, sun roki kasashen duniya kan abin da suke zargin zai faru da shi.

Dangin Kanu sun yi zargin cewa akwai shirin hallaka shi bayan kotu ta yanke masa hukuncin rai da rai a Abuja.

Ana zargin shirin hallaka Nnamdi Kanu a Sokoto
Shugaban IPOB da aka yankewa hukunci, Nnamdi Kanu. Hoto: Favour Michael Kanu.
Source: Twitter

Leadership ta ce kotun tarayya ta Abuja ƙarƙashin Mai shari’a James Omotosho ta kama Kanu da laifi kan tuhume-tuhume bakwai na ta’addanci tare da tura shi gidan yari.

Kara karanta wannan

An yi yunkurin kashe alkalin da ya daure Nnamdi Kanu? Kotun tarayya ta magantu

Hukuncin da aka yankewa Nnamdi Kanu

Wannan ya biyo bayan da alkalin ya yanke wa Kanu hukuncin daurin rai-da-rai kan tuhume-tuhume da dama na ta’addanci, tare da sassauta masa wasu saboda dalilai na jin kai.

An kuma bayyana cewa Kanu ya samu wani hukunci daban-daban kan laifukan kafa kungiya haramun da shigo da na’urar watsa shirye-shirye ba bisa ka’ida ba.

Kotu ta ce za a ci gaba da kula da shi a inda gwamnati ta amince, tare da hana shi amfani da na’urorin zamani ba tare da kulawar ofishin Nuhu Ribadu ba.

Kotu ta umurci hukumar DSS ta iya neman mallakar wasu kayayyaki da aka samo bayan kammala lokacin daukaka kara.

Ta kara da cewa Kanu bai nuna nadama ba, tana bayyana halayensa a matsayin rashin nuna ladabi, wadanda suka tabbatar da yiwuwar tashin hankali.

Dangin Nnamdi Kanu sun roki kasashen duniya
Nnamdi Kanu a cikin kotu yayin da ake shari'arsa. Hoto: Favour Michael Kanu.
Source: Facebook

Abin da iyalan Kanu ke zargi a Sokoto

Kara karanta wannan

Mutane sun ga abin da ba su taba gani ba bayan maida Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato

Kaninsa, Emmanuel Kanu, ya bayyana cewa sauya masa wurin zama daga ofishin DSS zuwa gidan gyaran hali na Sokoto na kunshe da makircin hallaka shi.

Ya zargi hukumomi da hana Kanu likitansa na musamman, yana mai cewa hakan na iya cutar da lafiyarsa da yake karɓar magani na musamman akai-akai.

Emmanuel ya ce komawa tsarin tsohon magani daga gwamnati barazana ce ga rayuwar Kanu, yana kiran duniya ta kula da abin da ke faruwa.

Ya jaddada cewa Nnamdi Kanu bai aikata laifin da ya cancanci wahala ko azaba ba, yana cewa ya nemi adalci ne ga mutanensa, cewar The Sun.

Iyalan sun roƙi ƙasashen duniya su daura alhakin duk abin da ya faru da Kanu a hannun jami’an tsaro. kan gwamnati da shugabanni.

Kanu: Kotu ta musanta yunkurin kashe alkali

Mun ba ku labarin cewa an yi ta yada labarin cewa wasu mutane sun yi yunkurin hallaka alkalin kotu da ya yi hukunci kan shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.

Kotun Tarayya ta yi karin haske kan labarin da ake yadawa kan Mai Shari'a, James Omotosho tana kira jama’a su watsar da labarin.

Kara karanta wannan

Shugaban DSS ya fadi halin tsaron da kasa ke ciki yayin ganawa da Tinubu

Hakan ya biyo bayan yankewa Kanu hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da laifin cin amanar kasa da ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.