An Yi Yunkurin Kashe Alkalin da Ya Daure Nnamdi Kanu? Kotun Tarayya Ta Magantu
- An yi ta yada labarin cewa wasu mutane sun yi yunkurin hallaka alkalin kotu da ya yi hukunci kan shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
- Kotun Tarayya ta yi karin haske kan labarin da ake yadawa kan Mai Shari'a, James Omotosho tana kira jama’a su watsar da labarin
- Hakan ya biyo bayan yankewa Kanu hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da laifin cin amanar kasa da ta'addanci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kotun Tarayya ta yi karin haske game da rahotanni da ake yadawa kan yunkurin kai harin domin hallaka alkalin da ya yi hukunci kan Nnamdi Kanu.
Kotun ta karyata rahoton cewa Mai Shari'a, James Omotosho ya tsira daga yunkurin kisa bayan hukuncin da ya yankewa Nnamdi Kanu.

Source: Twitter
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton Punch ya ce kotun ta bayyana labarin a matsayin karya tsagwaronta inda ta shawarci al'ummar Najeriya su yi watsi da rahoton.

Kara karanta wannan
Mutane sun ga abin da ba su taba gani ba bayan maida Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato
Hukuncin da aka yankewa Nnamdi Kanu
Wannan ya biyo bayan da alkalin ya yanke wa Kanu hukuncin daurin rai-da-rai kan tuhume-tuhume da dama na ta’addanci, tare da sassauta masa wasu saboda dalilai na jin kai.
An kuma bayyana cewa Kanu ya samu wani hukunci daban-daban kan laifukan kafa kungiya haramun da shigo da na’urar watsa shirye-shirye ba bisa ka’ida ba.
Kotu ta ce za a ci gaba da kula da shi a inda gwamnati ta amince, tare da hana shi amfani da na’urorin zamani ba tare da kulawar ofishin Nuhu Ribadu ba.
Kotu ta umurci hukumar DSS ta iya neman mallakar wasu kayayyaki da aka samo bayan kammala lokacin daukaka kara.
Ta kara da cewa Kanu bai nuna nadama ba, tana bayyana halayensa a matsayin rashin nuna ladabi, wadanda suka tabbatar da yiwuwar tashin hankali.
Yadda kotu ta karyata labarin yunkurin kisan alkali
Babban magatakarda, Suleiman ya ce kotu ta gano labarin daga wani mai amfani da shafukan sadarwa ne wanda ya yada shi ba tare da wata hujja ba.
Hassan ya ce wannan zargin babu tushe, kuma jama’a su guji yada shi domin kauce wa yada bayanan bogi, cewar Premium Times.
Ya bukaci hukumomin tsaro su binciki wadanda suka kirkire shi domin gano su da gurfanar da su kan laifukan cin mutunci da yaudara ta intanet.
Kotun ta yi gargadi cewa irin wannan labari na iya haifar da tsoro da kuma gurgunta amincewa ga tsarin shari’a.
An tsaurara tsaro a Sokoto saboda Nnamdi Kanu
A baya, kun ji cewa an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen gidan yarin Sokoto bayan labari ya bulla cewa an kai shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.
Wannan na zuwa ne bayan babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yanke wa jagoran 'yan aware hukuncin daurin rai da rai inda aka tura shi jihar.
Mazauna Sokoto sun bayyana cewa sun ga shigowar dakarun sojojin Najeriya da yawa, lamarin da suka ce ba su taba gani ba duk da matsalar tsaro da suke fama da ita.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
