Tinubu Ya Fadi Halin da Ya Shiga kan Matsalar Rashin Tsaro a Arewa

Tinubu Ya Fadi Halin da Ya Shiga kan Matsalar Rashin Tsaro a Arewa

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Najeriya musamman a yankin Arewa
  • Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gaji tarin dumbin matsalolin tsaro amma yana kokarin magance su
  • Shugaba Tinubu ya kuma nanata aniyarsa ta kawo karshen 'yan bindiga da 'yan ta'adda wadanda suka addabi yankin Arewa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce matsalar tsaro a Arewacin Najeriya ita ce babbar damuwarsa.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa matsalar rashin tsaron na barazana ga cigaban kasa da zaman lafiyar al’umma.

Shugaba Tinubu ya ce matsalar tsaro na damunsa
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ofis Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin bikin cikar shekaru 25 da kafa kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), ranar Asabar a birnin Kaduna.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: An taso Tinubu a gaba, malami ya buƙace shi don Allah ya yi murabus

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Tinubu ya ce kan rashin tsaro?

Shugaban kasan ya samu wakilcin shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, a wajen taron. Mai girma Tinubu ya ce gwamnatinsa ta gaji dimbin matsalolin tsaro masu sarkakiya, amma yanzu tana fuskantar su domin magance su.

“Babu abin da ke damuna fiye da rashin tsaro da ke addabar Najeriya, musamman Arewacin Najeriya. Matsalar da ta same mu a kowane yanki ta shafi kowa. Ba za mu bunƙasa ba idan wani ɓangare na kasar nan ya yi rauni."

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya ce ya gaji matsalar rashin tsaro

Shugaba Tinubu ya kara da cewa ya gaji kalubalen tsaro mai yawa, amma abin da ke ba ’yan ƙasa kwarin gwiwa shi ne yadda gwamnatinsa ke tunkarar matsalar cikin hanzari.

Ya ce yanzu ake bukatar muryoyi masu fadin gaskiya da jajircewa fiye da kowane lokaci a Arewa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan

Bayan fasa zuwa kasashen waje, ADC ta gayawa Tinubu abin da ya kamata ya yi

“Eh, an yi kura-kurai. Eh, akwai lokutan da aka shagala. Amma ba za mu ce Arewa ta gaza ba har sai idan mun daina zama 'yan uwan juna."
“Mun gaza ne ranar da muka kwanta lafiya alhali miliyoyin mutane suna kwana cikin yunwa, ranar da tsoro ya zama abokin tafiya daga gari zuwa gari.”

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya yi magana kan matsalar rashin tsaro
Shugaban kasar Najeriya, Mai girma Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Tinubu na son dawo da zaman lafiya a Arewa

Shugaban kasa ya sake nanata aniyar gwamnatinsa ta dawo da zaman lafiya da cigaba a Arewa, tare da kawar da ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke cutar da al’ummar yankin.

Ya kuma nuna kwarin gwiwa kan makomar Arewa, yana mai cewa yana fatan ganin ranar da tankokin daga Kolmani da sauran wuraren hakar mai na Arewa za su fara fita zuwa kasuwa.

Jam'iyyar ADC ta soki Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta soki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan matsalar rashin tsaro.

Jam'iyyar ADC ta kalubalanci Shugaba Tinubu da ya je jihar Kebbi kan daliban da aka sace domin ya nuna cewa ya damu da matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Hare haren 'yan bindiga ya ruguza lissafin Tinubu, ya tura wakili kasar Afirka ta Kudu

Hakazalika, ta soki matakin da ya dauki na fasa tafiyarsa zuwa kasae Afrika ta Kudu saboda halin rashin tsaro, inda ta ce hakan ba komai ba ne fa ce wasan kwaikwayo na siyasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng