Gwamnatin Tarayya Ta Rufe Duka Makaratu a fadin Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamnatin Tarayya Ta Rufe Duka Makaratu a fadin Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

  • Mutane na ta yada wani rahoto a kafafen sada zumunta cewa gwamnatin tarayya ta rufe dukkan makarantu a fadin Najeriya
  • Rahoton ya yi ikirarin cewa gwamnati ta dauki wannan matakin ne saboda tabarbarewar tsaro bayan sace dalibai a Kebbi da Neja
  • Ma'aikatar ilimi ta karyata wannan labari da ake yadawa, ta ce ba shi da tushe daga wata ma'aikata ko hukuma ta gwammati

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - An fara yada wani rahoto a kafafen aada zumunta cewa gwamnatin tarayya ta ba da umarnin kulle dukkan makarantu a fadin Najeriya saboda matsalar tsaro.

Rahoton wanda mutane ke ta yadawa ya yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ta bada umarnin rufe makarantun daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025.

Ministan ilimi, Tunji Alausa.
Hoton Ministan ilimi na Najeriya, Dr. Tunji Alausa Hoto: @DrTunjiAlausa
Source: Twitter

Ma'aikatar ilimi ta tarayya ta fito ta yi bayani kan gaskiyar lamarin a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Matawalle ya yi bayani bayan gano wurin da aka boye 'daliban da aka sace a Kebbi

Da gaske an rufe duka makaratun Najeriya?

Ma’aikatar Ilimi ta karyata wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an umarci a rufe makarantu a fadin Najeriya daga ranar 24 ga Nuwamba, 2025.

Ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya kuma mara tushe, tana mai jaddada cewa labarin ba daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi, ko wata hukumar Ilimi ta Jiha ko hukumomin tsaro da aka amince da su ya fito ba.

Sanarwar wacce Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta ma’aikatar ilimi, Folasade Boriowo, ta sanya wa hannu, ta yi kira ga jama’a da su daina dogaro da labari matukar ba daga gwamnati ya fito a hukumance ba.

Gwamnatin Tinubu ta ja hankalin jama'a

“Duk wata sanarwa, gargadi ko bayani da bai fito daga ingantaccen tushe ba, ya kamata mutane su yi watsi da shi domin ba abin dauka ba ne.
"Muna kira ga jama’a su tabbatar da sahihancin kowace magana kafin yada ta, domin dakile yaɗuwar bayanan ƙarya,” in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai

Ma’aikatar ta ja hankalin yan Najeriya cewa su daina daukar labari mara tushe, domin kaucewa yada abubuwan da haka suke ba.

Ta ce sanarwar da ta fito daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi, Gwamnatocin Jihohi da hukumomin tsaro da aka amince da su ne ya kamata a ɗauke su a matsayin sahihan bayanai.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana aiki a fadar shugaban kasa, Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Wadanne makarantu gwamnati ta rufe?

Wannan jawabin ya biyo bayan matakin da Gwamnatin Tarayya ta sanar ranar Juma’a na rufe makarantun Unity guda 47 da ke cikin yankunan da ake fama da rashin tsaro, sakamakon sace dalibai a jihohin Neja da Kebbi.

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu jihohi irinsu Kwara, Filato, Katsina da Neja suka rufe makarantu saboda ƙaruwa matsalar tsaro.

An rufe makarantu a jihar Katsina

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Dikko Umaru Radda ta umarci a rufe dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da ke fadin jihar Katsina.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da ma'aikatar kula da harkokin ilimin firamare da sakandire ta jihar Katsina ta fitar ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bada umarnin rufe makarantu 47 a fadin Najeriya

Ma'aikatar ta bayyana cewa an dauki wannan matakin ne saboda wasu dalilai da suka shafi tsaron al'umma a jihar Katsina.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262