Shugaban DSS Ya Fadi Halin Tsaron da Kasa ke ciki yayin Ganawa da Tinubu
- Shugaban DSS, Tosin Adeola Ajayi, ya yi wa shugaba Bola Tinubu bayani kan halin tsaro a daren Juma’a
- Hakan na zuwa ne bayan zafafa hare-hare da 'yan bindiga suka yi a jihohi da dama a kwanan nan
- ’Yan Najeriya sun mayar da martani, suna bukatar matakan gaggawa kan matsalar tsaro da ta addabi kasar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban hukumar DSS, Tosin Adeola Ajayi, ya yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu wani muhimmin bayani kan halin da kasa ke ciki game da tsaro.
Jawabin na zuwa ne bayan lamarin tsaro ya kara dagulewa musamman bayan sace dalibai a jihohin Kebbi da Niger.

Source: Facebook
Hoton zaman tattaunawar ya fito daga sakon da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Sace dalibai: An taso Tinubu a gaba, malami ya buƙace shi don Allah ya yi murabus
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganawar Tinubu da Ajayi ta jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya, inda jama’a da dama suka bukaci daukar matakai na gaggawa.
Dalilin zuwan shugaban DSS wajen Tinubu
Bayanin da Tosin Ajayi ya gabatar na zuwa ne kwanaki kadan bayan sace daliban makarantu a jihohin Kebbi da Niger, lamarin da ya kara tayar da hankali a fadin kasa.
Wannan ya sanya shugaban kasa ya soke tafiye-tafiye zuwa kasashen waje domin maida hankali kan tsaro, tare da tura ministocin tsaro zuwa yankunan da abin ya faru.
Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa shugaban kasa ya tura babban minista tsaro, Badaru Abubakar jihar Kebbi yayin da karamin ministan tsaro ya tafi jihar Kebbi.
Duk da cewa ba a bayyana abin da shugaban kasa ya tattauna da shugaban DSS ba, ana ganin zamansu na da nasaba da nazari kan nasarorin da kasa ke ciki.
Martanin ’yan Najeriya kan halin tsaro
Bayan sakin hoton shugaban kasa da Ajayi, 'yan Najeriya da dama sun yi martani a kafar X game da halin da kasa ke ciki.
Daga cikin masu mayar da martani akwai Atobajaye, wanda ya ce shugaban kasa yana kokari, amma kasar na fama da matsananciyar matsalar sace-sacen mutane.
Ya ce lokaci ya yi da ya kamata shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki mataki mai tsauri domin magance matsalar tsaro.
Shi kuwa A. Adebanji ya bayyana takaicinsa, yana cewa ana yin bayanin tsaro kullum ba tare da ganin wani canji ba.
Ya ce:
"Al’umma na rayuwa cikin tsananin fargaba, yayin da manyan jami’an gwamnati ke samun cikakken tsaro."

Source: Twitter
Wani mai suna Olla Idris ya ce ya kamata a rika yin bayanai kafin a kai hari ba bayan an yi barna ba.
Ya bukaci amfani da ingantacciyar fasaha, yana cewa dole a samu tsarin hoton tauraron dan Adam da ke bibiyar yanayin kasar gaba ɗaya.
An hana zanga-zanga a jihar Kebbi
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta gargadi wasu kungiyoyi da suka nemi yin zanga-zanga a jihar Kebbi.
Matasan sun ce za su yi zanga-zanga ne kan dalibai mata da aka sace a makarantar GGCSS Maga da ke karamar hukumar Wasagu.
Rundunar 'yan sanda ta ce zanga-zangar za ta iya kawo koma baya a kan kokarin ceto daliban da jami'an tsaro ke yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

