Bayan Fasa zuwa Kasashen Waje, ADC Ta Gayawa Tinubu Abin da Ya Kamata Ya Yi

Bayan Fasa zuwa Kasashen Waje, ADC Ta Gayawa Tinubu Abin da Ya Kamata Ya Yi

  • Jam'iyyar ADC mai adawa ta yi martani kan matakin da Bola Tinubu ya dauka na fasa tafiya zuwa kasashen waje
  • ADC ta bayyana cewa shugaban kasa ya yi hakan ne kawai domin ya nuna cewa ya damu da halin rashin tsaro
  • Ta bayyana abin da ya kamata Shugaba Tinubu ya yi idan har ya damu da abubuwan da ke faruwa na rashin tsaro

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta yi muhimmin kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Jam'iyyar ADC ta bukaci Shugaba Tinubu da ya ziyarci jihar Kebbi, inda 'yan bindiga suka sace dalibai mata 25 a kwanaki baya.

ADC ta ba Shugaba Bola Tinubu shawara
Shugaba Bola Tinubu da kakakin ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Mai magana da yawun ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi ne ya bayyana hakan yayin wata hira da jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Hare haren 'yan bindiga ya ruguza lissafin Tinubu, ya tura wakili kasar Afirka ta Kudu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya fasa zuwa Afrika ta Kudu

A ranar Juma’a, Shugaba Tinubu ya soke tafiyarsa zuwa Afrika ta Kudu da Angola saboda matsalolin tsaro a cikin kasar.

Sakamakon haka, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja domin wakiltar Najeriya a taron shugabannin kasashen G20 a birnin Johannesburg.

Hakazalika, Shettima zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron AU–EU da za a yi a Angola.

An tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da mai taimakawa mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Stanley Nkwocha, ya sanya wa hannu.

Meyasa Tinubu ya fasa tafiyar?

Dage tafiyar Shugaba Tinubu ya biyo bayan jerin munanan hare-hare da suka hada da, sace ɗalibai a Kebbi, hare-hare da sace mutane a cocin Eruku, jihar Kwara, sace wasu ɗalibai a makarantar St. Mary’s Catholic School da ke jihar Neja.

Shugaban kasa zai kasance a Abuja domin karɓar rahotanni daga manyan hafsoshin tsaro da kuma jagorantar ayyukan da ake gudanarwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda Jonathan ya ceto siyasar Najeriya da taimakonsa da ya yi

Ya kuma umurci hukumomin tsaro su kara tsananta bincike da aikin ceto, tare da karfafa matakan hana aukuwar hare-hare a yankunan da abin ya shafa.

Wane martani jam'iyyar ADC ta yi?

Sai dai mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana fasa tafiyar Shugaba Tinubu a matsayin wasan siyasa.

Jam'iyyar ADC ta soki Shugaba Tinubu
Mai magana da yawun ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter
“Ba shi da ma’ana. Siyasar wasan kwaikwayo ce kawai. Idan shugaban kasa ya ce ya tsaya saboda wadannan matsalolin, kun gan shi ya tafi Kebbi ko Kwara? Komai na wannan gwamnati wasan kwaikwayo ne da nuna iya magana."
"Idan yana son ya nuna ya damu, to ya nuna. Ya kamata mu ga ya je Kebbi. Shi ne babban kwamandan sojoji ba mataimakinsa ba."
"Idan zai tura mataimakinsa, me ya sa sai ya soke tafiyarsa? Ya je Kebbi domin ya tabbatar da cewa gaske ya damu."

- Bolaji Abdullahi

Gwamnatin Kebbi ta gano matsala

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta nuna yatsa ga hukumomin tsaro kan sace dalibai.

Gwamnatin ta bukaci samun bayanai daga gare su bayan an janye dakarun sojoji kafin 'yan bindiga suka harin da suka sace dalibai a wata makaranta.

Kara karanta wannan

PDP ta fara adawa mai zafi, ta ragargaji Tinubu kan sace dalibai a Kebbi

Ta bukaci su yi mata bayanin dalilin da ya sa aka janye sojojin duk da cewa an sanar da su kan yiwuwar kawo harin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng