Ta Ya Haka Ta Kasance: Gwamnatin Kebbi ta Gano Matsalar da Ta Auku kan Sace Dalibai
- Ana ci gaba da jimamin sace daliban da 'yan bindiga suka yi a wata makarantar sakandiren kwana a jihar Kebbi
- Gwamnatin jihar Kebbi ta nuna damuwa kan wata matsala da auku kafin 'yan bindiga su yi awon gaba da daliban
- Ta bukaci samun gamsashshen bayani daga wajen hukumomin tsaro domin gano dalilin aukuwar mummunan lamarin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya nemi bayanin gamsasshe daga hukumomin sojoji bayan sace dalibai.
Gwamna Nasir ya bukaci sanin dalilin janye dakarun da aka tura makarantar GGCSS Maga, kafin sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Joe Ajaero, ya kai ziyarar jaje ga jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me gwamnatin jihar Kebbi ta ce?

Kara karanta wannan
"Babu wurin zaman ƴan ta'adda a Kebbi": Gwamnati ta fadi yadda aka kai hari makaranta
Gwamna Nasir Idris ya ce lamarin ya tayar masa da hankali matuƙa saboda janye sojoji duk da cewa gwamnatin jihar ta bai wa jami’an tsaro rahoton sirri tun kafin faruwar harin.
A cewarsa, sojoji sun bar wurin ne kusan karfe 3:00 na dare, kuma maharan sun kai farmaki kusan minti 45 bayan haka.
“A matsayinmu na gwamnati mai lura da al’amura, mun kira taron tsaro bayan samun bayanan sirri na yiwuwar kai hari."
"Hukumomin tsaro sun tabbatar mana cewa babu damuwa, kuma za a tura jami’ai makarantar."
"An tura sojoji, amma daga bisani aka janye su da misalin karfe 3:00 na dare, sannan harin ya faru da karfe 3:45 na dare.”
- Gwamna Nasir Idris
Wace bukata Gwamna Nasir Idris ya nema?
Gwamnan ya kara da cewa jihar ta bukaci a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin janyewar dakarun.
“Wane ya ba da umarnin a janye sojoji? Ta yaya jami’an tsaro za su bar wurin a irin wannan lokaci na hadari?" "Wannan shi ne abin da ya dame mu. Mun bukaci a bincika kuma a gano wanda ya bayar da wannan umarni.”

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai
- Gwamna Nasir Idris
Gwamna Nasir Idris ya ce janyewar dakarun ya saba da alkawarin da hukumomin tsaro suka bayar na karfafa tsaro a makarantun yankunan kan iyaka da ’yan bindiga ke yawan kai hari, za a samu rahoton a The Punch.
Ana kokarin ceto dalibai a Kebbi
Ya ce gwamnati na aiki tukuru tare da gwamnatin tarayya domin ceto ’yan matan da aka sace.
“A matsayinmu na shugabanni, nauyinmu ne mu tabbatar da cewa ’ya’yanmu sun dawo gida cikin aminci, kuma muna yin duk abin da ya dace domin ganin hakan ta faru.”
- Gwamna Nasir Idris

Source: Facebook
Ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa tura mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, zuwa Kebbi, da kuma tabbatar da cewa karamin Ministan tsaro, Alhaji Bello Matawalle, ya koma Kebbi domin jagorantar ayyukan tsaro.
Gwamnan ya bayyana cewa an umurci malamai da limamai su kara yawaita addu’o’i domin dawo da waɗanda aka sace cikin koshin lafiya, tare da samun zaman lafiya na dindindin a jihar.
Dalilin Tinubu na kin zuwa Kebbi
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Uzor Orji Kalu, ya bayyana dalilin da ya sanya Shugaba Bola Tinubu bai je jihar Kebbi ba, bayan sace dalibai.
Sanata Kalu ya bayyana cewa Shugaba Tinubu bai je jihar Kebbi ba ne saboda hukumomin tsaro sun ba shi shawarar ka da ya je.
Kalu ya bayyana cewa shugaban kasa ya damu matuka kan sace daliban kuma ya yi umarnin a ceto su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
