'Yan Sanda Sun Ce ana Shirin Aikin da zai Dagula Kokarin Ceto Daliban Kebbi
- ’Yan sanda a Kebbi sun ce wasu kungiyoyi na shirin gudanar da zanga-zanga kan sace ’yan makarantar mata ta Maga da ke Wasagu
- Rundunar ta bayyana cewa zanga-zangar a wannan lokaci za ta iya dagula aikin ceto da jami’ai ke gudanarwa domin kubutar da daliban
- Hare-haren da aka kai makarantar sun jawo mutuwar mataimakin shugaban makarantar, Hassan Makuku, tare da dauke wasu dalibai mata
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi – Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta gargadi wasu ƙungiyoyi da ake zargin suna shirin gudanar da zanga-zanga biyo bayan sace daliban GGCSS Maga da aka yi.
Gargadin ya zo ne bayan samun bayanan sirri cewa ana shirin fitar da jama’a kan tituna domin nuna damuwa game da harin da ’yan bindiga suka kai a makarantar.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai

Source: Facebook
Rahoton Channels TV ya ce mai magana da yawun rundunar, Nafiu Abubakar, ya ce yanayin tsaro a jihar na da matuƙar hadari a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin satar daliban ya tayar da hankalin jama’ar yankin Danko/Wasagu, musamman yadda ’yan bindigar suka kashe mataimakin shugaban makarantar, Malam Hassan Makuku.
Gargadin 'yan sanda kan zanga-zanga a Kebbi
A cikin sanarwar, rundunar ta bayyana cewa kungiyar da ke shirin zanga-zangar ba ta yi shiri a lokacin da ya dace ba.
Punch ta rahoto cewa 'yan sanda sun bayyana cewa zanga-zangar za ta iya hana jami’an tsaro ci gaba da kokarin ceto daliban cikin ruwan sanyi.
Rundunar ta ce a lokacin da ake bukatar natsuwa da hadin kai, shiga titi ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Source: Twitter
’Yan sanda sun jaddada cewa suna aiki tare da sauran hukumomin tsaro, kuma suna cigaba da sintiri da kai dauki domin ganin an kubutar da daliban ba tare da wani lahani ba.

Kara karanta wannan
Bayan Kebbi da Neja, ƴan bindiga sun sace dalibai a Nasarawa? Ƴan sanda sun magantu
Yadda aka sace dalibai a jihar Kebbi
Wani shaidar gani da ido ya ce ’yan bindigar sun shigo makarantar ne ba tare da wata turjiya ba a lokacin sace daliban.
Rahotanni sun nuna cewa Malam Hassan Makuku ya yi ƙoƙarin kare dalibai ne suka harbe shi, lamarin da ya kara tayar da hankalin al’umma.
Jama’an yankin sun yi addu’o’i ga Makuku, suna rokon Allah ya gafarta masa, ya ji kansa, ya kuma ba iyalansa hakuri kan wannan rashi mai zafi da zalunci.
Gargadin ’yan sanda ga al’ummar Kebbi
A ƙarshe rundunar ta bukaci jama’a su guji duk wani abu da zai tayar da tarzoma, tare da kira gare su da su rika ba da sahihan bayanai ga ofishin ’yan sanda mafi kusa idan sun ga wani abu.
Rundunar ta ce tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne babban aikinta, kuma za ta ci gaba da yin hakan ba tare da gajiyawa ba.
Hanyoyin magance rashin tsaro a Najeriya
A baya mun kawo muku labari cewa mai sharhi kan lamuran tsaro, Audu Bulama Bukarti ya fadi wasu hanyoyin magance matsalar 'yan ta'adda a Najeriya.
Daga cikin hanyoyin da masanin ya kawo, Bukarti ya bukaci sanya ido a iyakokin Najeriya domin hana shigo da makamai da miyagun kwayoyi.
Ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu kan rashin tsaro ne tare da bayyana hanyoyin magance matsalar yayin da 'yan bindiga ke kara zafafafa hare hare a kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
