CAN: Dalibai da Malamai 227 'Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba da Su a Jihar Neja

CAN: Dalibai da Malamai 227 'Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba da Su a Jihar Neja

  • Kungiyar CAN reshen Neja ta tattara adadin dalibai da malaman da 'yan bindiga suka sace a makarantar Katolika da ke Papiri
  • Wannan hari da yan bindiga suka kai makarantar da tsakar dare ya tada hankulan mutane daga sassa daban-daban na kasar nan
  • Gwamnati da hukumomin tsaro sun sha alwashin cewa ba za su runtsa ba har sai sun tabbatar da ceto wadanda aka sace cikin koshin lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger, Nigeria - Bayan kwanaki da faruwar lamarin, an gano adadin daliban da 'yan bindiga suka sace daga makarantar Katolika a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bada umarnin rufe makarantu 47 a fadin Najeriya

Idan ba ku manta ba, a dare misalin karfe 2:00 na safiyar yau Juma'a, 'yan bindiga suka kai farmaki makarantar Katolika ta St Mary’s da ke Papiri, karamar hukumar Agwara a jihar Neja.

Makaranta.
Hoton kayan dalibai a makaran katolika a jihar Neja Hoto: Nagya Nupe
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta tattaro cewa maharan sun yi awon gaba da gomman dalibai tare da wasu daga cikin malamansu zuwa cikin daji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalibai nawa aka sace a jihar Neja?

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Neja ta bayyana cewa adadin dalibai da malaman da ke hannun 'yan bindiga bayan wannan mummunan al'amari.

CAN ta ce mutane 227 da suka kunshi dalibai da malamai ne 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su a harin da suka kai ba zato ba tsammani da tsakar dare.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daniel Atori, mai magana da yawun shugaban CAN na jihar Neja, Daniel Okoh,ya fitar da yammacin yau Juma'a, 21 ga watan Nuwamba, 2025.

Daniel Atori ya tabbatar da cewa “ɗalibai 215 tare da malamai 12” ne aka yi garkuwa da su a harin.

Wane kokari ake yi na ceto daliban Neja?

Kara karanta wannan

Wasu daliban da aka sace sun yi dabara, sun gudo daga hannun 'yan bindiga

Ya ce:

“Yanzu na dawo da daddare bayan na ziyarci makarantar, inda na kuma haɗu da iyayen yaran domin in tabbatar musu cewa muna aiki tare da gwamnati da jami’an tsaro domin ganin an ceto ’ya’yanmu lafiya.
“Daga bayanan da muka tattara, dalibai 215 da malamai 12 ne ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su.
“Ya kamata a lura cewa a lokacin harin ’yan ta’addan, wasu daga cikin daliban sun gudo sun dawo, kuma iyaye sun fara zuwa domin ɗaukar ’ya’yansu, domin dole ne a rufe makarantar.”
Yan sanda.
Hoton yan sanda a bakin aiki a Najeriya Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

CAN ta kwantar da hankulan jama'a

Atori ya kuma yi kira ga al'umma da iyayen yaran da aka sace su kwantar da hankulansu, tare da ba su tabbacin cewa jami'an tsaro na iya bakin kokarinsu, cewar Daily Post.

"Ina so in tabbatar muku cewa muna aiki kafada da kafada da jami’an tsaro, shugabannin al’umma da hukumomin gwamnati domin ganin an dawo da duk wanda aka sace cikin koshin lafiya," in ji shi.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Gwamnati ta bada umarnin rufe makarantu a fadin jihar Katsina

Wasu dalibai sun kubuta a Neja

A baya, kun ji labarin cewa an tabbatar da cewa wasu daga cikin daliban Katolika da 'yan bindiga suka sace daga makaranta a jihar Neja sun kubuta.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar da suka sace dalibai a makarantar Katolika sun zo da yawa, kuma sun isa makarantar a kan babura.

Ganau ya bayyana yadda maharan suka gamu da matsalar mota, wanda hakan ya sa wasu daga cikin daliban suka lallaba suka tsere.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262