An Kama Wasu daga cikin Ƴan Bindigan da Suka Kashe Kiristoci a Kwara? Gaskiya Ta Fito
- Rundunar ‘yn sanda ta karyata bidiyon da ya nuna cewa an kama ‘yan bindigar da suka kai hari wani cocin jihar Kwara
- Jami’an tsaro sun ce har yanzu babu wanda aka kama, yayin da ake ci gaba da aikin ceto wadanda aka sace a dazuzzuka
- Yayin da masana suka yi gargadi kan yada bidiyo ko labarai marasa tushe, mazauna Eruku sun bayyana halin da suke ciki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Rundunar ‘yan sandan Kwara ta yi martani kan wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke magana kan harin da aka kai wani coci a jihar.
Rundunar ta karyata cewa an kama wasu daga cikin ‘yan bindigan da suka kai hari a cocin Christ Apostolic da ke Eruku, a Karamar Hukumar Ekiti.

Source: Twitter
Bidiyon mai tsawon minti biyu da ya yadu a WhatsApp da Facebook, ya nuna cewa an cafke maharan cikin kasa da awa 48 bayan sun kashe masu ibada sun sace wasu, in ji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Ba a kama 'yan bindigan ba' - 'Yan sanda
Amma jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce babu kamshin gaskiya ko kadan a bayanan da ke cikin bidiyon.
A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, Ejire-Adeyemi ta bayyana a fili cewa har yanzu ba a samu damar kama ko da mutum daya ba da ake zargi da hannu a harin.
Ta ce jami’an tsaro sun bazama domin ci gaba da aikin ceto wadanda aka sace da kuma zakulo ‘yan bindigar da suka gudu zuwa dazuzzuka da ke kewaye da Eruku.
Ta kara da cewa:
“Rundunar ta na kira ga jama’a da su guji yada labarai ko bidiyoyi marasa tushe da za su iya haifar da tsoro ko kawar da tunanin jama'a.”
Mutane na cikin farga a yankunan Kwara
Har yanzu jama’a a Eruku da makwabtansu na cikin tsananin fargaba tun bayan harin da 'yan bindiga suka kai a yammacin Talata.
Wannan harin ya kara zama sabuwar barazanar tsaro a yankin da ya dade yana fama da hare-haren ‘yan bindiga a 'yan watannin nan.
Wasu shugabannin al’umma sun ce karuwar garkuwa da mutane da hare-hare daga ‘yan bindiga ya sa manoma da dama sun daina zuwa gonakinsu.
Wani mazaunin Eruku ya shaida wa jaridar Punch cewa:
“Har yanzu mutane suna cikin tsoro. An kawo mana hari ba zato ba tsammani, yanzu kuma wannan bidiyon da ake yadawa ya kara rikitar da jama’a. Abin da muke roko shi ne gwamnati ta gaggauta ba mu kariya.”

Source: Original
Masana sun fadi illar yada irin wannan bidiyo
Wani masanin tsaro na Ilorin, Taiwo Adeshina, ya ce matsalar yada bidiyoyi marasa inganci na zama babbar barazana ga shirin tsaro.
A cewarsa, hakan kan karkatar da hankali ko ya bata dabarun aikin jami’an tsaro, da kuma zaburar da su 'yan ta'addar.
“Dole ne mutane su koyi tantance labarai daga hukuma kafin su yarda. Karya a irin waɗannan lokuta na iya hana nasarar muhimman ayyuka.”
- Taiwo Adeshina.
'Yan bindiga sun kai sabon hari Kwara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai sabon hari kauyen Bokungi, karamar hukumar Edu ta jihar Kwara, inda suka sace manoma.
Wannan harin ya biyo bayan na garin Eruku a cikin kasa da awanni 24, lamarin da ya kara tsananta tsoro ga al'ummar Kwara.
Wani jami'in rundunar ƴan sanda ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa jami'an tsaro sun fara kokarin ceto manoman da aka sace a Bokungi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


