Tuhume Tuhumen da DSS Ke Yi wa Matashin da Ya Nemi a Kifar da Gwamnatin Tinubu

Tuhume Tuhumen da DSS Ke Yi wa Matashin da Ya Nemi a Kifar da Gwamnatin Tinubu

  • DSS ta gurfanar da mutum biyu a Abuja kan zargin laifuffukan ta’addanci da kuma neman kifar da gwamnatin Bola Tinubu
  • Daya daga cikin wadanda ake kara ya amince da aikata laifin tserewa daga kurkuku, amma ya ce bai aikata sauran laiffukan ba
  • Kotunan sun dage shari’o’in biyu zuwa 26 Janairu 2026, yayin da ake ƙara maida hankali kan yaki da ta’addanci a yanar gizo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Alhamis, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da wasu mutane biyu a gaban kotunan Tarayya dabam-dabam a Abuja.

An gurfanar da mutanen ne kan zarge-zarge masu nasaba da ta’addanci da kuma kiran juyin mulki ta hanyar kafafen sada zumunta.

DSS ta gurfanar da mutane 2 da ake zargi da aikata ta'addanci da neman juyin mulki
Wasu jami'an DSS a bakin aiki. Hoto: @OfficialDSSNG
Source: Twitter

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan DSS ta samu nasara a kotu, yayin da aka yanke wa wani babban kwamandan ISWAP hukuncin shekaru 20, in ji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta fadi halin kunci da ta shiga bayan sace dalibai mata a Kebbi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin Obadaki da kai hari cocin Okene

A karar farko, DSS ta gurfanar da Abdulmalik Abdulazeez Obadaki, wanda ake zargi da jagorantar harin cocin Deeper Life Bible a Okene, jihar Kogi, a shekarar 2012.

A wannan harin, an ce 'yan bindiga uku ne suka bude wuta a cocin, suka kashe akalla mutum 19, ciki har da shi kansa faston cocin, inji wata wallafa a shafin WikiPedia.

DSS ta gurfanar da Abdulmalik Obadaki gaban kotu bisa tuhume tuhume shiga, ciki har da:

  • Zama mamba na ƙungiyar ta’addanci
  • Yin makarkashiyar kai hari
  • Ba da taimako ga ayyukan ta’addanci
  • Ɓoye bayanai
  • Halartar ayyukan ’yan ta’adda
  • Tserewa daga hannun hukuma

Obadaki ya amince da aikata laifi guda ɗaya kacal — watau tserewa daga kurkuku — amma ya musanta aikata sauran tuhume-tuhume biyar.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Joyce Obehi, ta dage shari’ar zuwa 26 ga Janairu, 2026 domin duba lamarin da ya amince da shi tare da sauraron shaidu kan sauran laifuffuka.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun dawo, sun hana manoma taba amfanin gona sai da harajin miliyoyi

An gurfanar da matashi kan kiran juyin mulki

A wata kotun daban, DSS ta gurfanar da Innocent Chukwuemeka, wanda ake zargi da amfani da shafinsa na X (Twitter) wajen kira ga a kifar da gwamnatin Najeriya.

Ana tuhumarsa da aikata laifuffuka guda shida, ciki har da:

  • Wallafa bayanan ƙarya masu tayar da hankalin jama’a
  • Cin mutunci ta yanar gizo.

Chukwuemeka ya ƙi amincewa da dukkan zarge-zargen. Kotun ta dage shari’ar zuwa 26 ga Janairu, 2026, tare da bayar da umarnin a cigaba da tsare shi a hannun DSS.

Kotu ta dage sauraron kararrakin zuwa Disamba.
Harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: @FederalHigh
Source: UGC

Tserewar Obadaki daga kurkuku da hare-hare

Rahotanni sun nuna cewa Obadaki ya jagoranci harin bankuna guda biyar a Uromi, Edo, inda aka kashe mutane da dama kuma aka tafka babbar sata.

An tsare shi a gidan yarin Kuje, amma ya tsere yayin fashin magarkamar Kuje na 2022, wanda sama da fursunoni 600 suka tsere.

Daga baya ne hukumomin tsaro suka bayyana cewa Obadaki ne ya kitsa wannan fashin magarkama bayan da aka sauya masa wurin zama daga Kabba zuwa Kuje.

Kara karanta wannan

Duniya za ta kafa rundunar tsaro a Gaza, Falasdinawa za su iya samun 'yanci

DSS ta maida Nnamdi Kanu zuwa Sokoto

A wani labarin, mun ruwaito cewa, DSS ta tura Nnamdi Kanu zuwa gidan gyaran hali na Sokoto bayan kotun tarayya ta Abuja ta yanke masa hukunci.

Lauyansa Aloy Ejimakor ya tabbatar da matakin, yana cewa tura shi Sokoto ya nisanta shi da lauyoyinsa, iyalansa da kuma masoyansa.

Alkalin kotun ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai yayin da lauyar gwamnati ta nemi hukuncin kisa da katse na’urorin kafafen sadarwarsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com