Wasu Daliban da Aka Sace Sun Yi Dabara, Sun Gudo daga Hannun 'Yan Bindiga

Wasu Daliban da Aka Sace Sun Yi Dabara, Sun Gudo daga Hannun 'Yan Bindiga

  • An tabbatar da cewa wasu daga cikin daliban Katolika da 'yan bindiga suka sace daga makaranta sun kubuta
  • Ganau ya bayyana yadda maharan suka gamu da matsalar mota bayan sun kwashi dalibai cikin dare a jihar Neja
  • Gwamnatin Neja da rundunar yan sanda sun lashi takobin ceto duka daliban da aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu daga cikin daliban makarantar Katolika da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su sun gudo, sun dawo gida.

Idan za ku iya tunawa 'yan bindiga sun kai hari makarantar Katolika ta St. Mary’s da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara a Jihar Neja, inda suka sace dalibai da malamai.

Taswirar Neja.
Hoton taswirar jihar Neja a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa lamarin wanda ya tada hankulan jama'a ya faru ne misalin ƙarfe 2:00 na dare.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bada umarnin rufe makarantu 47 a fadin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun sace dalibai a Neja

Wannan na zuwa ne kwanaki huɗu kacal bayan irin haka ya faru a Jihar Kebbi, inda aka sace ɗalibai mata 25 daga makarantar sakandiren 'yan mata da ke garin Maga.

Rahotanni daga jihar Neja, sun nuna cewa 'yan bindigar da suka sace dalibai a makarantar Katolika sun zo da yawa, kuma sun isa makarantar a kan babura.

Wata sahihiyar majiya daga yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun fara harbi ne da isowarsu makarantar domin tsoratar da ɗaliban da duk wani jami’in tsaro da ka iya kasancewa a wurin, in ji Punch.

Yadda wasu dalibai suka kubuta

Ganau ya ce:

“Sun ci karensu ba babbaka na tsawon wasu sa’o’i ba tare da wani kalubale ba. Da farko, sun kwace mota, suka yi amfani da ita wajen ɗaukar ɗaliban, yayin da wasu suka tafi da su a kan babura.

Kara karanta wannan

Cocin katolika ya fadi halin da ake ciki bayan sace dalibai a Neja

"Sai dai motar da suka kwace suka yi amfani da ita wajen fitar da ɗaliban daga yankin ta lalace jim kadan bayan sun bar harabar makarantar, hakan ya sa suka ajiye ta a wurin.
“A lokacin da suka fara neman wata hanyar da za su samu mota don su tsere da ɗaliban, wasu daga cikin ɗaliban suka yi amfani da wannan dama suka gudu.
“Wasu ɗaliban kuma sun tsallake ta bayan katangar makarantar. Amma har yanzu ba mu tabbatar da adadin ɗaliban da aka sace ba."

Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Abubakar Usman, da rundunar ‘yan sandan jihar sun tabbatar da faruwar lamarin, suna mai cewa an ɗauki matakai domin ceto ɗaliban cikin koshin lafiya.

Gwamna Mohammed Umaru Bago.
Hoton Gwamna Umaru Bago a gidan gwamnatin jihar Neja Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Twitter

Sojoji sun kashe kwamandan yan bindiga

A wani labarin, kun ji cewa jiragen sojoji sun samu nasarar hallaka daya daga cikin manyan jagororin 'yan bindiga da suka addabi al'umma a jihar Neja.

An ruwaito cewa luguden wutan jiargen sojojin Najeriya ya hallaka Babangida, ɗaya daga cikin sanannun kwamandojin ’yan bindiga a karamar hukumar Shiroro.

Sai dai wani bayanin leken asiri ya nuna cewa sace ɗalibai da aka yi a wasu yankunan Kebbi da Neja kwanan nan na iya zama ramuwar gayya daga mayakan Babangida.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262