Hare Haren 'Yan Bindiga Ya Ruguza Lissafin Tinubu, Ya Tura Wakili Kasar Afirka ta Kudu
- A karshe dai shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya hakura da tafiya zuwa kasar Afirka ta Kudu domin halartar taron asashen G20
- Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Tinubu ya dauki wannan matakin ne domin maida hankali kan magance matsalar tsaron Najeriya
- Tinubu ya kuma tura mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, wanda tuni ya bar birnin Abuja zuwa kasar Afirka ta Kudu a yau Juma'a
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya - Yayin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya soke tafiyar da ya shirya yi zuwa kasar Afirka ta Kudu.
Shugaba Bola Tinubu ya fasa halartar halartar taron shugabanni na kasashen G20 wanda aka shirya yi a karshen makon nan da za mu shiga a Afirka ta Kudu.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya tura Shettima taron G20
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa maimakon haka, Bola Tinubu ya tura mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima domin ya wakilce shi a wannan taro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan bayani ya fito ne daga Stanley Nkwocha, Babban Mataimaki na Musamman ga Matakmakin Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa.
Nkwocha ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yanke shawarar ya zauna a cikin gida domin kula da matsalolin tsaro da suka taso a ƙasar nan.
Dalilin Tinubu na fasa zuwa Afirka ta Kudu
Ya ce Tinubu ya fasa tafiyar ne saboda karuwar karuwar hare-haren yan bindiga, musamman bayan abubuwan da suka faru kwanan nan a jihohin Kebbi da Kwara.
A cewarsa, saboda haka ne Tinubu ya yanke shawarar ya tura Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima a madadinsa.
Ya kara da cewa Mataimakin Shugaban Kasa ya riga ya tashi daga Abuja domin halartar taron shugabannin G20.
Yadda aka gayyaci Tinubu taron G20
A cewar sanarwar fadar shugaban kasa, an ji Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu, wanda shi ne shugaban taron G20 a wannan shekara, ne ya gayyaci Tinubu domin ya halarci taron bana.
An shirya gudanar da taron ne daga Asabar 22 ga Nuwamba zuwa Lahadi 23 ga Nuwamba, 2025 a Johannesburg Expo Centre da ke kasar Afirka ta Kudu.
Ana sa ran taron zai tattaro shugabannin manyan ƙasashe 20 masu cigaban tattalin arziki, ciki har da Tarayyar Turai, Kungiyar Tarayyar Afirka, da hukumomin kudi na duniya.

Source: Twitter
Tinubu ya soke shirye-shiryen tafiyar ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro suka ƙaru a Najeriya, lamarin da ya sa ya maida hankali wajen daukar matakan shawo kan lamarin.
Me ya hana Tinubu zuwa Kebbi?
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Orji Uzor Kalu ya ce hukumomin tsaro ne suka hana Shugaba Tinubu tafiya zuwa jihar Kebbi bayan sace dalibai 25 na makarantar GGCSS Maga.
Tsohon gwamnan na Abia ya kara da cewa Shugaba Tinubu ya soke wasu muhimman ayyuka da ya tsara a Afrika ta Kudu, Angola, da wasu kasashe domin ci gaba da zama a Abuja.
Sanata Kalu ya ce mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ziyarci Kebbi a madadin Tinubu, ya kuma dawo ya ba shi rahoton halin da ake ciki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

