Bayan Kebbi da Neja, Ƴan Bindiga Sun Sace Dalibai a Nasarawa? Ƴan Sanda Sun Magantu

Bayan Kebbi da Neja, Ƴan Bindiga Sun Sace Dalibai a Nasarawa? Ƴan Sanda Sun Magantu

  • Rundunar ’yan sanda ta yi martani kan labaran da ake yadawa na sace dalibai a makarantar St Peter’s a jihar Nasarawa
  • An gano daliban sun rikice ne bayan ganin mafarauta da bindigogi, lamarin da ya sa suka boye, har ake tunanin an sace su
  • Jami'an tsaro da aka tura cikin gaggawa sun tabbatar da cewa ba a sace dalibi ko daya ba, kuma makarantar ta yi bayani

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Rundunar ’yan sanda ta jihar Nasarawa ta yi watsi da rahotannin da ake yadawa cewa an sace dalibai biyu a makarantar St Peter’s Academy.

Legit Hausa ta fahimci cewa, makarantar St Peter’s Academy ta na garin Rukubi, karamar hukumar Doma da ke jihar Nasarawa.

Rundunar 'yan sanda ta ce ba a sace dalibai a makarantar Nasarawa ba
Babba sufetan 'yan sanda, IGP Kayode Egbetokun yana jawabi a wani taro a Abuja. Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

A sanarwar da aka wallafa a shafin X na 'yan sandan Nasarawa, an bayyana cewa laraban da ake yadawa na sace daliban karya ce tsagwaronta.

Kara karanta wannan

Cocin katolika ya fadi halin da ake ciki bayan sace dalibai a Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya faru a makarantar Nasarawa

Rahoton ya nuna cewa, labarin sace dalibai a Nasarawa ya sake jefa mutane a tsananin firgici, saboda an sace dalibai a Neja da Kebbi a kwanan nan.

A cewar kakakin rundunar, DSP Ramhan Nansel, sun samu kiran waya da misalin ƙarfe 10:00 na safe cewa wasu dalibai biyu sun ɓace yayin wasan motsa jiki a filin makarantar.

Bayan jin wannan, kwamishinan ’yan sanda na jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya tura tawagar jami’an ’yan sanda tare da sojoji zuwa yankin domin tantance gaskiyar lamarin.

Sai dai binciken farko ya tabbatar da cewa ba a sace yaran ba, sun gudu sun buya ne a wani waje da suka ga wasu mafarauta ɗauke da bindigogi, a tunaninsu 'yan bindiga ne.

Ba a sace dalibai a makarantar Nasarawa ba

Bayan an gundanar da binciken tsaro, jami’an sun gano cewa babu wani abu da ya faru a makarantar da za a iya kira garkuwa da mutane, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gwamna Bago ya fitar da bayanai bayan sace daliban makaranta cikin dare a Neja

A cewar rundunar, an yi bincike a yankin sosai, kuma an dawo da doka da oda, sannan hukumar makarantar ta ba da tabbacin cewa ba a sace dalibai ba.

Rundunar ta tabbatar da cewa yanzu haka an sanya yankin a karkashin sa ido na jami'an tsaro domin kauce wa duk wani yiwuwar barazana na tsaro.

'Yan sanda sun karyata rahotannin cewa an sace dalibai a jihar Nasarawa
Taswirar jihar Nasarawa. Hoto: Legit.ng
Source: Original

‘Yan sanda sun gargaɗi kafafen yada labarai

DSP Nansel ya yi kira ga jama’a da su guji yarda da bayanan da ba a tantance ba, yana mai gargadin kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da ingancin labari kafin wallafawa.

Ya ce yawaitar wallafa rahotanni marasa tushe na iya tayar da hankalin jama’a da kuma kawo cikas ga aikin jami’an tsaro da ke wurin.

Karanta sanarwar a nan kasa:

'Yan bindiga sun sace dalibai a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai wani babban harin a Papiri, jihar Neja, inda suka afka makarantar St Mary’s Catholic.

Majiyoyi da dama sun shaida cewa har yanzu babu takamaiman adadin dalibai ko ma’aikatan da aka yi garkuwa da su, inda makarantar ke kan tattara bayanai.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake shiga makaranta sun sace dalibai da malamai a Neja

Jami’an tsaro daga rundunoni daban-daban sun fara aikin ceto daliban da aka sace, tare da bincike a dazukan da ke kewaye da yankin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com