Sace Dalibai: Sojojin Najeriya Sun Hallaka Kwamandan 'Yan Bindiga a Jihar Neja

Sace Dalibai: Sojojin Najeriya Sun Hallaka Kwamandan 'Yan Bindiga a Jihar Neja

  • 'Daya daga cikin kwamandojin 'yan bindiga kuma na hannun daman jagoran 'yan ta'adda, Dogo Gide ya bakunci lahira a jihar Neja
  • Kasurgumin dan ta'addan mai suna Babangida ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu a farmakin jiragen sojoji a yankin Shiroro
  • Kisan Babangida ya raunana dabar Dogo Gide, kuma ana ganin shi ya jawo hare-haren sace dalibai a Neja da Kebbi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Rundunar Sojojin Saman Najeriya na ci gaba da luguden wuta kan 'yan ta'adda da nufin kawar da duk wani bara gurbi da dawo da zaman lafiya a Najeriya.

A wannan karon, jiragen sojoji sun samu nasarar hallaka daya daga cikin manyan jagororin 'yan bindiga da suka addabi al'umma a jihar Neja.

Jirgin sojin sama.
Hoton jirgin yakin rundunar sojojin saman Najeriya Hoto: @NAF
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa luguden wutan jiargen sojojin Najeriya ya hallaka Babangida, ɗaya daga cikin sanannun kwamandojin ’yan bindiga a karamar hukumar Shiroro.

Kara karanta wannan

"Ba ƴan ta'adda ba ne": An gano ƴan bindigan da suka kai hari jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan ta'addan na daya daga cikin jagorori kuma na hannun daman kasurgumin dan bindigar nan, Dogo Gide.

Sojoji sun kashe aminin Dogo Gide

Wata majiya mai ƙarfi ta ce Babangida ya mutu ne a ranar 18 ga Nuwamba, 2025 sakamakon raunukan da ya samu a harin da jiragen yakin sojoji suka kai yankin ƙauyen Kurebe, inda aka kashe ’yan ta’adda da dama.

Majiyar ta ce mutuwar Babangida ta raunana dabar Dogo Gide, wanda ya shahara wajen kai hare-hare masu tsanani a sassan Jihar Neja da makwabtan jihohi.

Sai dai wani bayanin leken asiri ya nuna cewa sace ɗalibai da aka yi a wasu yankunan Kebbi da Neja kwanan nan na iya zama ramuwar gayya daga mayakan Babangide.

A ranar 19 ga Nuwamba, shugabannin al’umma daga Kwaki, Buresidna, Chukuba, Buwidna, Kuchidna, Banda da Shalupe sun ziyarci Palleli, gidan mahaifiyar Dogo Gide, inda aka ga tana alhinin rashin amintaccen kwamandan ɗanta.

Kara karanta wannan

Bayan kashe Kiristoci a coci, ƴan bindiga sun sake kai hari Kwara, sun sace mutane

Kisan Babandiga ya raunana yan bindiga

Wani babban jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"Kisan Babangida babban nasara ne da ta girgiza sansanin su, amma hakan na iya haifar da ƙarin hare-haren ramuwar gayya kan fararen hula da jami’an tsaro.”

Ya kara da cewa an ankarar dukkan hukumomin tsaro domin dakile duk wani yunkurin kai hari da kuma kare al’ummomin da ke cikin haɗari, in ji Daily Post.

Jami'an sojoji.
Hoton dakarun sojoji a cikin daji a Najeriya Hoto: @NigeriaArmy
Source: Facebook

Wata majiya daga Hedikwatar NAF ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa rundunar za ta ci gaba da hare-hare kan yan ta'adda da dakile yunkurinsu na ramuwar gayya.

Sojoji sun yi luguden wuta a Sambisa

A wani labarin, kun ji cewa dakarun rundunar sojin saman Najeriya sun kai farmaki kan sansanin ‘yan Boko Haram a cikin dajin Sambisa, jihar Borno.

Rundunar sojin ta tabbatar da cewa dakarun Operatiom Hadin Kai ne suka kai wannan faramaki, kuma sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama.

Kara karanta wannan

Trump: Gwamnati ta 'dora alhakin karuwar ta'addanci a Najeriya a kan shugaban Amurka

Wannan farmakin ya nuna cewa sojin sama na ci gaba da kasancewa cikin shiri wajen kare kasar nan da tallafa wa sojojin kasa da ke fafatawa a fagen fama.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262