Kungiyar CAN Ta Yi Magana bayan Sace Dalibai a Niger, Ta ba Kiristoci Shawara
- Kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Niger ta yi magana game da harin da yan bindiga suka kai a daya daga cikin makarantun Kiristoci
- CAN ta la’anci harin da ‘yan bindiga suka kai St. Mary’s Papiri, inda aka sace dalibai, malamai da ma’aikacin tsaro
- Kungiyar ta ce harin ya faru tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 3:00 na dare, inda ‘yan ta’adda suka shiga makarantar, suka harbi mai gadi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minna, Niger - Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Niger ta yi martani kan sace dalibai da malamai a jihar.
Kungiyar ta yi Allah-wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai makarantar St. Mary’s da ke Papiri a jihar wanda ya yi sanadin sace dalibai.

Source: Original
Niger: CAN ta yi Allah-wadai da sace dalibai
A wata sanarwa da shugaban kungiyar ya fitar wanda Channels TV ta samu, shugaban Rabaran Bulus Yohanna ya bayyana takaici kan harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yohanna ya bayyana cewa harin ya hada da sace wasu malamai da ma’aikatan tsaro da aka dauke da ƙarfi.
Ya kara da cewa lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 1:00 na dare zuwa 3:00 na dare, ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce:
“Shugaban CAN na jihar Niger Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, yana sanar da cewa wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun mamaye St. Mary da ke Papiri, karamar hukumar Agwarra a jihar Niger.
“Lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 3:00 na daren Juma’a, 21 ga Nuwamba 2025, inda suka yi garkuwa da dalibai, malamai da kuma wani ma’aikacin tsaro da suka harbe.
“CAN ta yi tir da wannan mummunan hari tare da nuna damuwa kan lafiyar yaran da aka sace da iyalansu."
Yohanna ya tabbatar wa jama’a cewa cocin na aiki tare da jami’an tsaro, shugabannin al’umma da hukumomin gwamnati domin ceto wadanda aka sace.

Source: Facebook
Rokon da CAN a Niger ta yi ga al'umma
Shugaban, wanda shi ma Fasto ne a cocin Kontagora ya roki jama’a da su kwantar da hankali, su taimaka wa hukumomi, tare da ci gaba da addu’a domin dawo da yaran cikin koshin lafiya.
“CAN na nan daram wajen kare ‘ya’yanmu, kuma za ta rika sanar da karin bayani idan an samu tabbacin sahihancin rahotanni.
“Mu roki Ubangiji ya kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, kuma ya ci gaba da kiyaye jama’arsa daga dukkan hadurra.”
- Kungiyar CAN
Rahotanni sun ce maharan sun kutsa makarantar ne a yankin Agwara da sassafe inda suka yi barna, cewar rahoton Punch.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun zo da yawa, kan babura fiye da 60 tare da wata mota, suka kai harin.
An ce sun harbi mai gadin makarantar, wanda yanzu haka yake dauke da munanan raunuka.
Cocin Katolika ya magantu kan sace daliban Niger
Mun ba ku labarin cewa Cocin Katalika a jihar Niger ya tabbatar da harin da yan bindiga suka kai a daya daga cikin makarantun Kiristoci tare da kwashe yara da malamai.
Majiyoyi sun bayyana cewa an sace daliban a safiyar ranar Juma'a, 21 ga watan Nuwambar 2025, lamarin da ya kara gigita mazauna Arewacin Najeriya.
Harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan sace daliabi a wata makaranta da ke jihar Kebbi, tare da kashe mataimakin shugaban makarantar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


