Abu Ya Girma: Gwamnati Ta bada Umarnin Rufe Makarantu a fadin Jihar Katsina

Abu Ya Girma: Gwamnati Ta bada Umarnin Rufe Makarantu a fadin Jihar Katsina

  • Jihohin Arewa na ci gaba da daukar matakan da suke ganin sun dace domin kare rayukan dalibai da malamai a makarantun gwammati
  • Hakan na zuwa ne bayan hare-haren da 'yan bindiga suka kai tare da sace dalibai da malamai a makarantu a jihohin Neja da Kebbi
  • Gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko Radda ta bi sahu, inda ta ba da umarnin rufe duka makarantun da ke karkashinta nan take

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Yayin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a Arewacin Najeriya, gwamnatin Katsina ta fara daukar matakan bai wa jama'arta kariya a makarantu.

Gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda ta umarci a rufe dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da ke fadin jihar Katsina.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
Hoton Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da ma'aikatar kula da harkokin ilimin firamare da sakandire ta jihar Katsina ta fitar yau Juma'a, kamar yadda The Nation ta kawo.

Kara karanta wannan

Matawalle ya yi bayani bayan gano wurin da aka boye 'daliban da aka sace a Kebbi

An rufe makarantu a jihar Katsina

Ma'aikatar ta bayyana cewa an dauki wannan matakin ne saboda wasu dalilai da suka shafi tsaron al'umma a jihar Katsina, kamr yadda Leadership ta rahoto.

Ma’aikatar ta ja hankalin iyaye, malamai da al’umma gaba ɗaya da su bi wannan umarnin nan take, yayin da ake ci gaba da bibiyar yanayin tsaron jihar baki ɗaya.

A cewarta, gwamnatin Katsina na ci gaba da bibiya da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da kare rayuwar ɗalibai da ma’aikata a fadin jihar.

Hare-haren da suka jijjiga Najeriya

Wannan mataki na zuwa ne bayan wasu 'yan bindiga sun kutsa cikin makarantar Katolika a jihar Neja, sun sace dalibai da malamai.

Harin ya zo ne kwanaki kadan bayan 'yan bindiga sun sace dalibai 'yan mata daga makarantar sakandiren mata ta gwamnati da ke garin Maga a jihar Kebbi.

Wadannan hare-hare da 'yan bindiga suka kai sun tayar da hankula, lamarin da ya aa jihohin da ke makwaftaka suka fara daukar matakai domin kare dalibai da ma'aikata.

Kara karanta wannan

Shugaban Amurka, Trump ya kara daukar zafi, ya kira Najeriya da kalma mara dadin ji

Dalilin rufe makarantu a jihar Katsina

Sakamakon haka ne, gwamnatin Katsina ta hannun ma'aikatar ilimin firamare da sakandire ta umarci rufe makarantun gwamnati a duka kananan hukumomi 34 na jihar.

"Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta Jihar Katsina ta umarci rufe dukkan makarantun gwamnati da ke faɗin jihar saboda dalilai na tsaro.
"Ta ja hankalin iyaye, malamai da al’umma da su bi wannan umarnin nan take, yayin da ake ci gaba da bibiyar yanayin tsaron jihar baki ɗaya don kare rayuwar ɗalibai da ma’aikata," in ji ranarwar.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
Hoton mai girma gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Wani malamin makaranta a karamar hukumar Danja, Abubakar Abdullahi ya tabbatar wa Legit Hausa cewa sun samu sakon wannan mataki kuma sun sanar da dalibai.

Ya ce dama jarabawar karshen zangon karatu na farko za a fara makon gobe, amma kuma rayuwa da lafiya su na gaba da komai, don haka suna goyon bayan gwamnati.

"Tsaro matsala ce da ta shafi kowa, kuma ita lafiya da rayuwa su ne farko a kowane irin lamari, duk da hakan zai taba kalandar karatu amma lamari ne da ya shafi tsaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai

'Fatan mu Allah Ya kawo mana zaman lafiya, muna rokon Allah Ya taimaki sojojin mu da ke yaki da wadannan mutane, ya ba su nasara ta yadda za mu koma a ci gaba da karatu," in ji shi.

Gwamnati ta rufa makarantu a Kwara

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kwara ta bada umarnin rufe dukkanin makarantu kananan hukumomi hudu saboda karuwar tsaro a jihar.

Gwamnati ta ba da wannan umarnin rufe makarantun ne ta hannun kungiyar malamai ta NUT reshen jihar Kwara a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba.

Ta bukaci dukkanin makarantun da ke kananan hukumomin hudu su bi wannan umarni cikin gaggawa domin umarni ne kai tsaye daga Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262