Bidiyon Nnamdi Kanu Yana Rusa Kuka a Kotu Ya Ja Hankalin Jama'a

Bidiyon Nnamdi Kanu Yana Rusa Kuka a Kotu Ya Ja Hankalin Jama'a

  • Bidiyon Nnamdi Kanu yana kuka a kotu yayin da za a yanke masa hukuncin ya jawo muhawara a kafafen sadarwa
  • Reno Omokri ya ce wannan shi ne karon farko da ya ga shugaban kungiyar 'yan ta'addan IPOB yana rusa kuka
  • ’Yan Najeriya da dama sun yi martani daban-daban kan bidiyon, daga kira ga adalci zuwa fassarori kan hukuncin kotu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bidiyon da ya nuna jagoran kungiyar 'yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu, yana kuka a cikin kotu ya haifar da mahawara mai zafi a shafukan sada zumunta.

Wannan bidiyo ya bayyana ne jim kadan bayan kotun tarayya da ke Abuja ta yanke masa hukuncin da ya haɗa da daurin rai da rai.

Nnamdi Kanu a kotun tarayya a Abuja
Nnamdi Kanu kafin yanke masa hukunci a kotu. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Tsohon mai ba wa shugaban kasa shawara, Reno Omokri, ne ya yada bidiyon a Facebook, yana mai cewa wannan shi ne karo na farko da ya ga Kanu yana kuka.

Kara karanta wannan

An kama wasu daga cikin ƴan bindigan da suka kashe Kiristoci a Kwara? Gaskiya ta fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan lamari ya sa jama’a da dama suka fara bayyana ra’ayoyinsu kan hukuncin, halin Kanu, da kuma yadda tsarin shari’a ke tafiya a Najeriya.

Kotun ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai a kan tuhumomi na 1, 4, 5 da 6 da suka shafi aikata ta’addanci, tare da hukuncin shekaru 20 kan tuhuma ta 3 da kuma shekaru 5 kan tuhuma ta 7.

Bidiyon yadda Kanu ya yi kuka a kotu

Bidiyon wanda ya karade dandalin intanet ya nuna Nnamdi Kanu cikin yanayi na bakin ciki da kunci a cikin kotu.

Reno Omokri ya rubuta cewa bidiyon ya bayyana wani bangare na Kanu da ba a saba gani ba, yana rokon Allah ya taimaka masa a wannan mawuyacin hali da ya samu kansa a ciki.

Hakan ya sa jama’a da dama fara taƙaddama kan ko ya dace a tausaya masa ko kuma a mai da hankali kacokan kan shari’ar da aka masa.

Kara karanta wannan

Birnin Shehu ya yi baƙo, DSS ta maida Nnamdi Kanu Sokoto, zai zagaye Najeriya

Martanin 'yan Najeriya kan kukan Kanu

Daya daga cikin masu sharhi, Olu Olabode, ya yi gargadin cewa bai kamata kukan ya rinjayi binciken gaskiya da neman masa adalci ba.

Ya ce dole ne a ci gaba da kallon lamarin da idon basira domin kauce wa son zuciya da rashin daidaito a tsarin shari’a.

Tajudeen Okunlola ya ce:

“Duk da ba na son bakin ciki ko wahalar da wani ɗan adam kamar ni zai shiga… amma idan aka duba da tunani mai kyau, ina ganin an masa abin da ya dace da shi domin bai taɓa nuna nadama ba a lokacin gurfanarsa a kotu.”

Lukman Shehu ya ce:

“Suna kiransa zaki, amma zaki ba ya kuka kamar kare da ya ji rauni, sai dai rugugi na musamman!”

Solomon Masev fatan nasara ya yi wa Kanu da cewa:

“Zai dawo ya zama shugaban kasa na farko ɗan kabilar Igbo bayan Nnamdi Azikiwe.”

Strides comedy ya ce:

“Reno Omokri, yanzu kana da damar ka yi masa ba’a, amma ka sani cewa watarana zai rama.”

Kara karanta wannan

'Daurin rai da rai': Cikakken hukuncin da kotu ta yanke wa Kanu, shugaban IPOB

Reno Omokri a wani taro
Reno Omokri da ya saka bidiyon Kanu yana kuka. Hoto: Reno Omokri
Source: Facebook

Kanu ya birkita zaman kotu a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban 'yan ta'addan IPOB ya birkita zaman kotun tarayya a ranar Alhamis da ta wuce.

Nnamdi Kanu ya yi magana yana ihu tare cewa alkalin bai san doka ba bayan an ki amincewa da wata bukatarsa.

Bayan hargowar da Nnamdi Kanu ya yi, alkalin kotun ya umarci jami'an tsaro da su yi waje da shi kafin a yanke masa hukunci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng