Cocin Katolika Ya Fadi Halin da ake ciki bayan Sace Dalibai a Neja

Cocin Katolika Ya Fadi Halin da ake ciki bayan Sace Dalibai a Neja

  • Cocin katalika da ke jihar Neja ya tabbatar da cewa wasu mahara sun kai farmaki daya daga cikin makarantun kiristoci tare da kwashe yara da malamai
  • Labarin harin ya bayyana a safiyar ranar Juma'a, 21 ga watan Nuwamban 2025, lamarin da ya kara gigita mazauna Arewacin Najeriya
  • Harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan sace daliabi a wata makaranta da ke jihar Kebbi, tare da kashe mataimakin Shugaban makarantar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Nigier – Cocin Katolika ta Kontagora ta tabbatar da cewa wasu ’yan bindiga sun kai hari a makarantar St. Mary da ke Papiri a jihar Neja.

Sanarwar da cocin ya fitar a ranar Juma'a ta ce maharan sun sace ɗalibai, malamai da wani jami’in tsaro a safiyar ranar 21 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake shiga makaranta sun sace dalibai da malamai a Neja

Cocin katolika ta tabbatar da sace daliban Neja
Gwamna Muhammad Umaru Bago, Gaban makarantar St. Mary da ke Papiri Hoto: Niger state/Legit.ng
Source: Facebook

A cikin sanarwar da wani Temilola Sobola ya wallafa a shafin Instagram ta bayyana cewa wannan harin da ya faru cikin dare ya daga hankali a al’ummar da ke yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kai hari makaranta a Neja

Daily Post ta wallafa cewa a sanarwar hukuma da cocin ta fitar, ta ce maharan sun kai harin ne tsakanin 1.00 na dare zuwa 3.00 na safe, lamarin da ya jefa ma’aikata da ɗalibai cikin firgici.

Sanarwar ta ce wani jami’in tsaro da ke bakin aiki ya samu munanan raunuka sakamakon harbin da maharan suka yi masa.

An fara neman daliban Neja da aka sace
Gwamnan jihar Neja, Muhammad Umaru Bago Hoto: Niger State
Source: Original

Sanarwar cocin ta ce:

“Babban damuwa shi ne a kan tsaron rayukan yaran da aka yi garkuwa da su da kuma iyalansu."

Ta ƙara da cewa an sanar da jami’an tsaro nan take, kuma sun fara aikin hadin gwiwa domin ceto waɗanda aka sace lafiya lau.

Jami'an tsaro sun bazama dazukan Neja

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Tinubu ya umarci Matawalle ya tattara kayansa ya koma Kebbi

Sanarwar ta kara da cewa hukumomin tsaro da suka hada da 'yan sanda da sojoji sun shiga dazuka yankin da kewaye domin gano inda aka tafi da ɗaliban.

An tabbatar da cewa jami'an tsaron suna aiki tare da shugabannin al’umma da jami’an gwamnati domin tabbatar da an fitar da yaran cikin koshin lafiya.

Cocin ta nemi jama’a su kwantar da hankulansu, su ci gaba da ba hukumomin tsaro hadin kai, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare yaran da ke karkashinta.

Sanarwar ta ce:

“Diyosisi na kira ga jama’a su zauna lafiya, su tallafa wa jami’an tsaro, tare da cigaba da addu’a domin gaggawar dawo da duk wadanda aka sace.”

Cocin ta sha alwashin ci gaba da fitar da karin bayani yayin da sahihan rahotanni ke shigowa kan yara da malaman da aka kwashe.

Ta'addanci: An dauki mataki a Kano

A baya, kun samu labarin cewa gwamnatin Jihar Kano ta ƙara himma wajen karfafa tsaro a fadin jihar bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya mikawa rundunar JTF sababbin motoci da babura.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Sanatan Amurka ya taso gwamnati a gaba kan sace dalibai a Kebbi

Gwamnan ya bai wa jami’an JTF motoci 10 da babura 50, lamarin da ake sa ran zai taimaka wajen hanzarta kai dauki da kuma saurin isa wuraren da manyan motocin tsaro ba sa iya shiga.

Sanarwar ta fito ne daga mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya bayyana cewa wannan na daga cikin aikin gwamnati na tsaron rayuka da dukiyoyi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng