Rundunar Sojoji Za Ta Tilasta wa ’Yan Najeriya Shiga Aikin Soja? Gaskiya Ta Fito

Rundunar Sojoji Za Ta Tilasta wa ’Yan Najeriya Shiga Aikin Soja? Gaskiya Ta Fito

  • Rundunar sojojin Najeriya ta fitar da sanarwa, domin wayar da kan al'umma kan jita-jitar cewa za ta tilasta wa matasa shiga aikin soja a kasar
  • An danganta jita-jitar da cewa Laftanar-janar Waidi Shuaibu ne ya yi ikirarin tilasta matasa shiga soja, sai dai rundunar ta fito ta yi bayani
  • Sanarwar da rundunar ta fitar ta jawo martani daga jama’a, inda wasu suka nemi sojoji su maida hankali kan matsalolin tsaro da ya addabi mutane

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta fitar da sanarwa domin wayar da kan 'yan Najeriya kan yada jita-jita game da daukar sababbin sojoji a kasar.

Rundunar ta ce fitar da sanarwar ta zama dole inda ta yi karin haske kan cewa wai za ta tilasta yan Najeriya shiga aikin soja.

Kara karanta wannan

Muhawara ta raba 'yan majalisar Amurka 2 kan zargin kashe Kiristoci a Najeriya

Sojoji sun karyata tilasta matasa shiga aikin soja
Hafsan sojojin Najeriya, Laftanar-janar Waidi Shuaibu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Legit Hausa ta samu wannan sanarwa ne daga shafin rundunar wanda ta wallafa a manhajar X a yau Juma'a 21 ga watan Nuwambar shekarar 2025 da muke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karairayi da ake yadawa kan hafsan sojoji

Hakan ya biyo bayan yada cewa wai rundunar tana shirin tilasta wa matasa a Najeriya shiga aikin ko da ba su so.

A rahoton da ake yadawa wanda shafin The Academy Regulars ya wallafa a Facebook, an ce idan har matasan Najeriya suka ki shiga aikin soja a kasar, to rundunar za ta saka su da karfi da yaji.

Har ila yau, labarin da ake yadawa ya ce wai za a tilasta matasa daga shekaru 18 zuwa sama idan har ba su shiga aikin ba.

An danganta wannan bayani da cewa sabon hafsan sojojin kasar, Laftanar-janar Waidi Shuaibu da aka ba mukamin kwanan nan ne ya fada,

Kara karanta wannan

Za a dauki sojoji 24,000 a Najeriya domin gamawa da 'yan ta'adda

A labarin, an ce Waidi Shuaibu ya ce dakarun sojoji har guda 10,000 da suka dauka a bara sun bace a ribibi saboda haka akwai bukatar wasu.

Rundunar sojoji ta ƙaryata cewa za ta tilasta matasa shiga aikin soja
Hafsan sojoji da darakunsa a bakin fama. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Martanin wasu yan Najeriya kan sakon sojoji

Wannan martani na rundunar sojoji ya jawo martani da dama daga yan Najeriya musamman masu ta'ammali da kafar sadarwa ta X.

Mafi yawan wadanda suka yi martani sun yi cikin raha da cewa ai da an gwada yin haka saboda tuni suka riga suka fara motsa jiki saboda aikin kasa.

Wasu ko cewa suke yi ba wannan ne a gaban mutane ba, ya kamata su fitar da sanarwa kan sace dalibai, kashe soja a Borno da sauran matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Za a dauki sojoji 24,000 a Najeriya

A baya, kun ji cewa shugaban rundunar sojin ƙasa ya bayyana shirin ɗaukar sababbin sojoji domin ƙara ƙarfin dakaru a fadin ƙasa gaba daya saboda yaki da ta'addanci.

A cewar rundunar, sababbin cibiyoyin horo uku za su samar da sojojin da ke da cikakkiyar kwarewa a fagen yaƙi wanda zai taimaka sosai wurin inganta tsaro.

Kara karanta wannan

An 'gano' jihohi 8 da 'yan ta'adda za su iya kai mummunan hari a Najeriya

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da kalubalen tsaro a yankuna da dama domin tabbatar da gamawa da yan ta'adda ba tare da bata lokaci ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.