Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Matakan Tsaro a Kano bayan Sabunta Hare Hare a Jihohi

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Matakan Tsaro a Kano bayan Sabunta Hare Hare a Jihohi

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da sababbin motoci da babura domin inganta aikin dakarun JTF a Kano da kewaye
  • An ce hakan zai inganta tsaro da karfin aiki musamman a kananan hukumomin da ke fuskantar barazana
  • Gwamnan Kano ya jaddada kudirin gwamnatinsa na bai wa tsaro fifiko a dukkan sassan kananan hukumomin jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta kara himma wajen karfafa tsaro a fadin jihar bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya mikawa rundunar tsaro ta JTF kayan aiki.

Gwamnan jihar ya ba jami'an JTF sababbin motoci 10 da babura 50 domin inganta ayyukan tsaro a Kano.

Motoci da baburan da aka raba a Kano
Motoci da baburan da gwamnatin Kano ta ba JTF. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Sanarwar ta fito ne daga mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa a wani sako da ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna Bago ya fitar da bayanai bayan sace daliban makaranta cikin dare a Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka mika wa JTF motoci a Kano

Taron mika motoci da baburan ya gudana a fadar shugaban gwamnati da ke Kano, inda manyan jami’an tsaro da shugabannin kananan hukumomi suka halarta.

A cewar gwamnati, motocin da baburan za su taimaka wajen bunkasa kai dauki da kuma samun damar shiga wuraren da manyan motocin ba za su iya shiga ba.

Amfanin raba motoci da baburan

Sanarwar ta bayyana cewa motoci 10 da babura 50 da aka ba JTF za su taimaka wajen inganta yawan wuraren da jami’an tsaro za su iya kula da su.

An ce kayan aikin sun fi karkata ga kananan hukumomin Kiru, Tsanyawa, Kunchi, Ghari, Shanono, Tudun Wada da Doguwa, wadanda ake ganin suna bukatar karin kulawa kan batun tsaro.

Rahotani sun ce jami'in gwamnatin Kano, Umar Baba Zubairu ne ya mika takardar rarraba wadannan kayayyaki a madadin Manjo Janar Sani Muhammad (mai ritaya).

Kara karanta wannan

Gurbatar ruwa: An gano babban hadarin da ke tunkaro mutane a Kebbi da jihohi 2

A yayin bikin, wikilin shugaban JTF, AM Tukur ne ya karbi motoci da baburan kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna.

Jami'an tsaron da suka halarci taron

Wakilan kwamishinan 'yan sanda, daraktan DSS, kwamandan NSCDC sun halarci taron mika kayayyakin.

Haka zalika shugabannin kananan hukumomin Kiru, Tsanyawa da Gwarzo sun shaida taron da kansu.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin wani taro. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wannan, kamar yadda sanarwar ta ce, ya nuna hadin kai tsakanin hukumomi daban-daban da ke da alhakin tabbatar da tsaron jihar.

Masu lura da lamura sun bayyana cewa karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi da gwamnati irin wannan yana da matukar tasiri wajen kawo karshen kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta.

Gwamna Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace domin samar da kariya ga dukkan al’ummar Kano.

'Yan bindiga sun sace dalibai a Neja

Kara karanta wannan

Kiraye kiraye sun yawaita, ana son Tinubu ya yi murabus daga shugabancin Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Neja ta tabbatar da sace dalibai a wata makarantar kwana a daren Juma'a.

Hakan na zuwa ne bayan wasu 'yan bindiga sun sace dalibai mata a wata makaranta a jihar Kebbi a makon nan.

Gwamnatin Neja ta yi Allah wadai da sace daliban tare da bayyana cewa ta riga ta gargadi makarantar kafin kai harin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng