Yan Bindiga Sun Sake Shiga Makaranta Sun Sace Dalibai da Malamai a Neja

Yan Bindiga Sun Sake Shiga Makaranta Sun Sace Dalibai da Malamai a Neja

  • Rahotanni sun ce an sace dalibai da ma’aikata da ba a tantance adadinsu ba a makarantar St. Mary’s da ke Neja
  • An ce ’yan ta’adda sun kutsa makarantar ne da misalin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na dare, yanzu ana tantance abin da ya faru
  • Lamarin ya biyo bayan sace dalibai a wata makarantar mata a Kebbi da rufe makarantu da dama a Kwara cikin mako guda

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

A Jihar Neja - Wasu ’yan bindiga sun kai farmaki makarantar St. Mary’s School da ke Papiri, karamar hukumar Agwara a jihar Neja.

'Yan ta'addan sun yi awon gaba da dalibai da ma’aikata da ba a san adadinsu a lokacin hada wannan rahoton.

Makarantar da aka sace dalibai a Neja
Kofar makarantar da yan bindiga suka sace dalibai a Neja. Hoto: Legit
Source: Original

Legit ta samu bayanai cewa harin ya haifar da firgici a yankin, musamman ma a cikin iyayen yara da dama.

Kara karanta wannan

Karfin hali: 'Yan bindiga sun nemi kudin fansa har Naira biliyan 3 a Kwara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi daga cocin Katolika da ke jihar sun tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai sun ce suna kan tattara cikakkun bayanai.

Wani babban jami’i na karamar hukumar Agwara ya tabbatar da harin a cikin wani jawabi ta waya, yana mai cewa jami’an tsaro da ma'aikatan na ci gaba da tantance bayanai.

Karin bayani kan daliban da aka sace

Majiyoyi da dama sun shaida cewa har yanzu babu takamaiman adadin dalibai ko ma’aikatan da aka yi garkuwa da su, domin makarantar na kan tattara bayanai cikin gaggawa.

Wata majiya daga cocin Katolika ta cewa jaridar Daily Trust:

“Eh, gaskiya ne, amma ba ni da hurumin fadin cikakkun bayanai. Coci zai fitar da sanarwa daga baya.”

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Neja ya ce za su fitar da bayanai idan sun kammala bincike bayan an tuntube shi.

Wannan batu ya ƙara tabbatar da cewa hukumomi ba su da cikakken bayani, musamman ganin cewa harin ya faru tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na dare.

Kara karanta wannan

Gwamna Bago ya fitar da bayanai bayan sace daliban makaranta cikin dare a Neja

Gwamnan jihar Neja
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago yana jawabi. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Twitter

Maganar sace dalibai a jihar Kebbi

Harin da aka kai a Neja ya faru ne kwanaki kaɗan bayan sace dalibai 25 a makarantar Maga da ke Jihar Kebbi, abin da ya jefa al’ummar yankin Arewa maso Yamma a wani yanayi.

Lamarin ya haifar da tambayoyi masu ƙarfi kan yadda makarantun yankin ke ci gaba da fuskantar barazana tare da karuwar rashin tsaro.

A Jihar Kwara kuwa, mahukunta sun rufe makarantu sama da 50 sakamakon yawaitar hare-haren ’yan bindiga da suka shafi kauyuka da makarantu.

Wannan mataki ya nuna yadda matsalar tsaro ta fadada zuwa makarantu, inda yara da malamai ke kara fadawa cikin haɗari.

Bayanin da gwamna Umaru Bago ya yi

A wani labarin, kun ji cewa gwamna Umaru Bago ya fitar da sanarwa game da sace dalibai da aka yi a jihar Neja.

Gwamna Bago ya ce tun a karon farko an bukaci makarantun kwana da ke yankin Neja ta Arewa su rufe saboda barazanar tsaro.

Kara karanta wannan

Asiri ya bankadu: An kama magidanci yana neman sulalewa da gawar matarsa a babur

Ya kara da cewa a yanzu haka an umarci jami'an tsaro da su gaggauta kokari wajen ceto daliban cikin koshin lafiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng