Maharan ISWAP Sun Afkawa Jami'an Tsaro, An Kashe Ɗan Sanda a Yobe
- Ƴan ta'addan kungiyar ISWAP sun kai wani mummunan hari jihar Yobe, a karamar hukumar Ministan Ƴan sanda, Ibrahim Geidam
- ’Yan ta’addan sun ƙona motoci biyu na sintiri da jami'an ƴan sanda ke amfani da ita, yayin da suka tafi da guda ɗaya a Geidam din
- Rahotanni sun nuna cewa bayan harin da suka kai Geidam, ƴan ta'addan na taruwa na taruwa a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Yunusari
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Yobe – Wasu 'yan ta'adda da ake zargin cewa mayakan ISWAP ne sun kai hari kan jami'an ’yan sanda da ke Geidam a Jihar Yobe, mahaifar tsohon gwamna kuma Ministan yan sanda, Ibrahim Geidam.
Rahotanni daga wurin sun nuna cewa maharan sun ƙona motocin sintiri guda biyu sannan suka ƙwace guda ɗaya yayin harin da ya ɗauki kusan mintuna 45.

Kara karanta wannan
Bayan kashe Kiristoci a coci, ƴan bindiga sun sake kai hari Kwara, sun sace mutane

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa majiyar tsaro ta ce maharan sun iso wurin kusan karfe 1.30 na dare a ranar Laraba, inda suka bude wuta a kan bayin Allah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ISWAP ta kashe dan sanda a Yobe
Trust radio ta wallafa cewa mayakan ISWAP sun kashe wani jami'in dan sanda a yayin da suka bi dare wajen kai hari kan jami'an tsaro a jihar Yobe.
Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa:
“Maharan sun kashe ɗan sanda ɗaya, suka buɗe ɗakunan da ake tsare masu laifi, suka ƙona motocin sintiri biyu sannan suka tafi da wata mota ɗaya.”
Majiyar ta ƙara da cewa bayanan leken asiri sun nuna cewa mayakan ISWAP suna taruwa a wasu yankuna na ƙaramar hukumar Yunusari.
Majiyar ta ce:
“Rahotanni masu inganci sun ce 'yan ta'adda na tattaruwa a Sukdu, Buhari, Mattati da Bulabulin."
'Yan sanda sun tabbatar da harin ISWAP
Da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan
Trump: Gwamnati ta 'dora alhakin karuwar ta'addanci a Najeriya a kan shugaban Amurka
Ya bayyana cewa maharan sun kai hari a kan jami'an tsaron ne kila domin su yi awon gaba da motoci, amma yanzu haka aka kan binciken lamarin.

Source: Original
Hare-haren ta’addanci sun ƙara ƙamari a sassan ƙasar nan, lamarin da ya sanya Shugaba Bola Tinubu dage wasu tafiye-tafiyen ƙasashen waje.
A makon da ya gabata, ’yan ta’adda sun kashe sojoji, jami’an CJTF da wani Birgediya Janar, a ranar Litinin, ’yan bindiga sun afka makarantar GGCSS da ke Maga, a Jihar Kebbi.
Bayan kwanaki biyu, wasu maharan sun yi wa cocin Kwara tsinke, inda suka kashe wasu masu ibada kuma suka yi garkuwa da mutum 30.
Mayakan ISWAP sun kai hari Borno
A baya, kun ji rahotanni daga jihar Borno sun ce mayakan kungiyar ISWAP sun kai sabon hari a garin Mayenti, lamarin da ya jawo asarar rayuka da kuma tsananta fargaba a yankin.
Harin ya faru ne a daren Litinin, awanni bayan kungiyar ta ISWAP ta saki bidiyon da ke nuna kisan Birgediya Janar M. Uba, babban jami’in sojin kasar nan da mayakanta suka kama.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kashe malamin addini, sun sace masu ibada a Kwara
Majiyoyin tsaro sun ce mayakan ISWAP sun kutsa cikin garin ne da daruruwan babura, inda suka yi musayar wuta da dakarun soji na tsawon lokaci, lamarin da ya jawo asarar rayuka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng