Abu Ya Girma: An Kai Karar Najeriya ga Majalisar Dinkin Duniya kan ‘Kisan Kiristoci’

Abu Ya Girma: An Kai Karar Najeriya ga Majalisar Dinkin Duniya kan ‘Kisan Kiristoci’

  • Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Michael Waltz, ya kai karar Najeriya kan “kisan dubban Kristoci” a kasar
  • Waltz ya kai korafin ne ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya domin daukar matakai da suka dace bayan zarge-zarge
  • Ya yi kira ga Najeriya ta dauki mataki kan sace ’yan mata 25 a Kebbi, yana mai cewa dole ne gwamnati ta kara tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Michael Waltz, ya koka kan karuwar ta'addanci a Najeriya.

Waltz ya gabatar da rahoto ga kwamitin tsaro na Majalisar kan abin da ya kira kisan gilla ga dubban Kiristoci a Najeriya.

Ambasadan a Amurka ya kai karar Najeriya
Shugaba Donald Trump da Bola Tinubu. Hoto: Donald J Trump, Bayo Onanuga.
Source: Getty Images

A cikin wani faifan bidiyo da ofishin jakadancin Amurka ya wallafa a X, Waltz ya bayyana damuwa kan kashe-kashen da ake yi.

Kara karanta wannan

Faston da ya fara maganar kisan Kiristoci ya sake bayyana a gaban majalisar Amurka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asarar da ta'addanci ya jawo a Najeriya

Har ila yau, Waltz ya koka kan kona kauyuka da kuma harin da ake kai wa shugabannin coci a yankunan da rikice-rikice suka dabaibaye.

Ya ce hare-haren Boko Haram da ISIS sun ci gaba da hallaka rayuka tare da barin dimbin asara.

Ya kuma ambaci sace dalibai mata 25 a jihar Kebbi inda jami’in makarantar ya rasa ransa yayin kokarin kare yaran daga ’yan bindiga.

A cewarsa, Amurka na matukar damuwa da “kisan Kristoci” da ake zargi kungiyoyi da ta’addanci a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

Waltz ya ce ana kashe matasan coci da mazauna kauyuka ne “saboda sun yi imani da Kiristanci ko kuma ikirarin bada gaskiya ga Yesu Kristi.

Jakadan ya yi nuni da cewa har yanzu gidaje da kauyuka na ci gaba da salwanta, yayin da manyan makamai ke yawo.

Kara karanta wannan

Muhawara ta raba 'yan majalisar Amurka 2 kan zargin kashe Kiristoci a Najeriya

Ya koka da cewa abin da ke faruwa na takaici ne kuma ba zai taba karbuwa ba duba da zubar da jini da ake yi.

Ana ci gaba da kalubalantar Najeriya kan zargin kisan Kiristoci
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Bukatar Amurka kan zargin kisan Kiristoci

Waltz ya ce Amurka na bukatar ganin an dauki mataki kai tsaye, ya yi nuni da maganar shugaban Amurka Donald Trump, yana mai cewa kasar ba za ta zuba ido ba yayin da irin wannan tashin hankali ke faruwa a Najeriya.

Ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta kara tsaro, ta magance matsalolin da ke haifar da tashin hankali da kuma tabbatar da cewa masu aikata laifuka sun fuskanci hukunci.

A baya-bayan nan, Trump ya saka Najeriya cikin jerin “Kasashen da ake da damuwa kansu” bisa zargin kisan Kristoci, zargin da Najeriya ke musantawa.

Kiristoci: Wasu yan majalisar Amurka sun magantu

An ba ku labarin cewa wata daga cikin ’yar majalisa a Amurka, Sara Jacobs, ta yi magana game da barazanar da Donald Trump ya yi wa Najeriya.

Sara ta yi magana ne a zaman sauraron zargin da aka yi wa Nigeria. Jacobs ta ce ɗaura tashin hankalin da ake yi kan addini bai bayyana ainihin matsalar kasar ba.

Kara karanta wannan

Ribadu da manyan Najeriya sun isa Amurka, sun tattauna batun rashin tsaro

Wani ɗan majalisar Amurka, Brian Jack, ya soki duk wani yunƙuri na tura sojojin Amurka Najeriya, yana cewa hakan zai sake jawo matsaloli.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.