Trump: Wasu 'Yan Majalisar Amurka Sun Yi Matsaya kan kai Hari Najeriya

Trump: Wasu 'Yan Majalisar Amurka Sun Yi Matsaya kan kai Hari Najeriya

  • ’Yar majalisar dokokin Amurka, Sara Jacobs, ta yi magana game da barazanar da Donald Trump ya yi wa Najeriya ta kai hari don kare Kiristoci
  • A zaman sauraron zargin da aka yi wa Nigeria Jacobs ta ce ɗaura tashin hankalin da ake yi kan addini bai bayyana ainihin matsalar kasar ba
  • Wani ɗan majalisar Amurka, Brian Jack, ya soki duk wani yunƙuri na tura sojojin Amurka Najeriya, yana cewa hakan zai sake jawo matsaloli

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – A cigaba da mahawara kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya, ’yar majalisar dokokin Amurka daga jihar California, Sara Jacobs, ta soki shugaba Donald Trump.

Sara Jacobs ta soki barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan batun aikewa da sojojinsa don kare Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Fafaroma ya magantu kan zargin kisan Kiristoci, ya tsage gaskiya

Donald Trump, Sara Jacobs
Trump da Sara Jacobs da ta masa martani kan kai hari Najeriya. Hoto: @RepSaraJacobs|Getty Images
Source: Twitter

Rahoton Channels TV ya ce 'yar majalisar ta yi magana ne ne yayin da ake zaman sauraron rahotanni kan zargin da Trump ya yi wa Najeriya a majalisar dokokin Amurka.

Jacobs, wacce ke cikin kwamitin harkokin ketare, ta ce maganganun Trump na iya janyo mummunan tasiri, domin rikice-rikicen Najeriya sun shafi Musulmi da Kiristoci baki ɗaya.

Martanin Sara kan barazanar Trump

A yayin zaman sauraron rahoton, Sara Jacobs ta bayyana cewa ɗaura dukkan tashin hankalin da ake yi a Najeriya kan addini ba zai magance matsalar ba.

Ta ce:

“Barazanar da Trump ya yi abu ne na ganganci. Yunƙurin kai farmakin soja a Najeriya ba ya kan ƙa’ida. Majalisar dokoki ba ta amince da amfani da soja don kare Kiristoci a Najeriya ba.”

Ta ƙara da cewa Najeriya na fama da kalubalen tsaro da ya shafi addinai biyu, don haka akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta ƙara kaimi wajen kare rayukan al’ummar ta daga ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan

'Kai makaryaci ne': Yar siyasar Canada ta zagi ministan Tinubu, ya yi martani mai zafi

Sara Jacobs ta ce tura sojojin wata ƙasa ba zai kawo mafita ba, illa ƙara dagula tsaro da fargaba a yankin.

Jack bai yarda da tura sojoji Najeriya ba

A nasa bangaren, wani ɗan majalisar wakilai na Amurka, Brian Jacks, ya yi tsokaci mai zafi, yana cewa yunƙurin tura rundunar soji Najeriya “mataki ne da zai sa a tuna da mulkin mallaka.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yana sa hannu a wata takarda. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa ya ce:

“Ban amince da duk wani shiri na tura sojojin Amurka Najeriya ba. Wannan mataki ne mai hatsari da ka iya farfado da damuwowin mulkin mallaka a nahiyar Afirka.”

Ya yi nuni da cewa Amurka ba ta nuna irin wannan damuwa lokacin da rikicin Sudan da na DR Congo suka yi kamari ba, don haka tsoma baki a Najeriya ba zai zama abin da ya dace ba.

Ya ci gaba da cewa:

“Ba a kawo zaman lafiya a Afirka da makamai ko tura soja. Ana kawo zaman lafiya ne da gina makarantu, samar da ruwan sha, habaka tattalin arziki da kuma haɗin kai.”

Kara karanta wannan

Ribadu da manyan Najeriya sun isa Amurka, sun tattauna batun rashin tsaro

Tawagar manyan Najeriya ta je Amurka

A wani labarin, kun ji cewa wata tawaga ta musamman daga Najeriya ta isa kasar Amurka game da zargin da Donald Trump ya yi wa kasar.

Tawagar ta gana da dan majalisar Amurka mai yada farfagandar cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne ya jagoranci tawagar da ta kunshi hafsun tsaro da sufeton 'yan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng