Magana Ta Kare: Fafaroma Ya Magantu kan Zargin Kisan Kiristoci, Ya Tsage Gaskiya

Magana Ta Kare: Fafaroma Ya Magantu kan Zargin Kisan Kiristoci, Ya Tsage Gaskiya

  • Fafaroma Leo XIV ya sake yin magana game da zargin cewa ana yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla a Najeriya
  • Ya ce Musulmai da Kiristoci duka suna fuskantar kisan gilla a Najeriya, yana danganta matsalar da ta’addanci da rikicin tattalin arziki
  • Rahotanni sun nuna rikicin ya shafi batun ƙasa, talauci, da rikice-rikicen manoma da makiyaya, ba wai addini kaɗai ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Rome, Italy - Fafaroma Leo XIV ya bayyana damuwa kan karuwar ta'addanci a Najeriya inda ya fadi musabbabin matsalolin.

Fafaroma ya bayyana cewa Musulmai da Kiristoci duka an yi musu kisan gilla a Najeriya, inda ya ce matsalar tana da nasaba da ta’addanci da rikicin tattalin arziki.

Fafaroma ya magantu kan zargin kisan Kiristoci
Shugaba Bola Tinubu da Fafaroma Leo XIV. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Fafaroma ya yi maganar ne yayin da yake barin gidansa na Castel Gandolfo, inda ya amsa tambayar da aka yi masa kan tsaron Kiristoci a Najeriya, cewar EWTN Vatican.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Tinubu ya umarci Matawalle ya tattara kayansa ya koma Kebbi

Zargin Amurka kan matsalar tsaron Najeriya

A gefe guda, Amurka ta ayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai babbar matsalar cin zarafin ‘yancin addini.

Donald Trump ya yi barazanar daukar matakin soji idan har ba a kawo karshen kisan gilla da ya ce ana yi wa Kiristoci ba.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta cewa rikicin ƙasar yana da alaka da addini, tana mai cewa masu tayar da hankali na kai hari kan wanda ya ƙi bin akidar su, ko Musulmi ko Kirista.

Martanin Fafaroma kan zargin kisan Kiristoci

Leo XIV ya ce tabbas a wasu yankuna akwai barazana sosai ga al'ummar Kiristoci amma ya ce lamarin ya shafi har da Musulmi.

Ya ce:

“A wasu yankuna na Najeriya akwai barazana ga Kiristoci, amma ga kowa ma gaba ɗaya. Duka Kiristoci da Musulmai ana kashe su.”

Ya ƙara da cewa akwai matsala ta ta’addanci, kuma akwai rikici mai nasaba da tattalin arziki da kuma rikicin mallakar ƙasa, ya nemi gwamnati ta inganta sahihin ‘yancin addini ga jama’a, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Kai makaryaci ne': Yar siyasar Canada ta zagi ministan Tinubu, ya yi martani mai zafi

Fafaroma ya yi wannan jawabi ne bayan ya shafe rana a Villa Barberini sannan ya koma Vatican, inda matasa da ma’aurata masu shirin aure suka tarbe shi da murna tare da mika masa hotonansu.

Trump ya zargi ana kashe Kiristoci a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump na Amurka. Hoto: Donald J Trump, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Fasto ya jawo magana kan rashin tsaron Najeriya

Cardinal Pietro Parolin ma ya jawo ce-ce-ku-ce bayan da ya ce tashin hankalin Najeriya ba rikicin addini ba ne, illa rikicin zamantakewa tsakanin makiyaya da manoma.

Rahoton Punch ya ce masu sukar wannan matsayi sun ce hakan na rage nauyin wahalar da Kiristoci ke sha musamman a yankin Arewa ta Tsakiya.

Wasu rahotanni suka ce duk da cewa Kiristoci na fuskantar hare-haren kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi, Musulmi ma ba su tsira ba saboda kungiyoyin ba su yin bambanci lokacin kai hari.

Gwamna Kirista ya karyata kisan Kiristoci

Kun ji cewa Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya fito da bayanai a kan zargin cewa ana ware Kiristoci saboda addininsu a Najeriya.

Ya bayyana cewa rikice-rikicen da ake fama da su ba su kai matsayin da za a kira sukisan kare dangi ba, kuma ya karyata batun jihadi a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yadda mutuwar Gaddafi a Libya ke ci gaba da zama barazana ga Najeriya'

Alia ya ce ya yi bayani kai tsaye ga jakadan Amurka domin kore rahotannin da ba su da tushe na cewa Najeriya kasa ce da ke kashe K-iristoci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.