'Daurin Rai da Rai': Cikakken Hukuncin da Kotu Ta Yanke wa Kanu, Shugaban IPOB

'Daurin Rai da Rai': Cikakken Hukuncin da Kotu Ta Yanke wa Kanu, Shugaban IPOB

  • Wata babbar kotu a Abuja ta samu Nnamdi Kanu da laifuffukan ta’addanci, ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai tare
  • Mai shari'a, James Omotosho, ya kafa tsauraran sharuddan zaman Kanu a gidan yari, ciki har da hana shi amfani da waya
  • Kotun ta kuma kwace dukkan na’urorin watsa shirye-shirye na IPOB da Radio Biafra, don dakile tada fitina da kiyaye tsaron kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – An samu cikakken hukuncin da Mai shari'a James Omotosho na babbar kotun tarayya a Abuja ya yanke wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Kotun ta samu Nnamdi Kanu da laifuffuka masu alaka da ta’addanci, wadanda ta ce sun yi barazana ga tsaron ƙasa da zaman lafiyar jama’a.

Kotu ta yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai saboda laifuffukan ta'adanci.
Shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a cikin babbar kotun tarayya. Hoto: @YeleSowore
Source: Twitter

A hukuncin da aka yanke, kotun ta ce akwai gamsasshiyar hujja cewa Kanu ya yi jerin jawabai tare da watsa shirye-shirye da suka tayar da tarzoma, kisan jama’a da bayar da umarnin kai hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar, in ji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

‘A duba tsufansa’: 'Dan majalisa ya roki alkali ya sassauta hukuncin Nnamdi Kanu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikakken hukuncin kotu kan Nnamdi Kanu

A hukuncin da ya karanto, Mai shari'a Omotosho ya bayyana cewa, an yanke wa Kanu hukuncin:

  • Daurin rai-da-rai a kan tuhume-tuhume na 1, 4, 5 da 6, wadanda suka shafi ta’addanci kai tsaye.
  • Shekaru 20 a kurkuku kan tuhuma ta 3.
  • Shekaru 5 a kurkuku kan tuhuma 7, ba tare da zabin biyan tara ba.

Za a aiwatar da dukkanin hukunce-hukuncen zaman gidan yarin a lokaci guda. Yayin da yake karanta hukuncin, alkalin ya ce:

“Girman laifuffukan da kuma illarsu ga tsaron kasa ya sa ba za a iya kawar da kai a kansu ba. Dole ne doka ta yi aikinta.”

Tsauraran sharuɗɗan tsare Kanu a gidan yari

Kotun ta ce Kanu ba zai sake komawa gidan yari na Kuje ba, saboda yadda ya rika nuna halin tashin hakali a lokacin shari'ar, maimakon haka kotu ta yanke cewa:

  • Za a tsare Kanu a cikin ‘wani kurkuku’ mai tsananin tsaro.
  • An haramta masa amfani da duk wata na’urar zamani kamar waya ko kwamfuta.
  • Idan akwai bukatar amfani da na’ura, dole ne ya samu izinin kai tsaye daga mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro (NSA) tare da tsauraran kulawa.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Kotu ta yankewa Nnamdi Kanu hukunci bayan samunsa da laifi

Jaridar The Punch ta rahoto Mai shari'a Omotosho ya na cewa:

“Wadannan matakai suna da muhimmanci domin hana kara tayar da fitina da tabbatar da zaman lafiyar kasa.”
Kotu ta ba da umarnin a kwace na'urorin POB da Radio Biafra bayan yanke wa Kanu hukunci.
Shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a cikin babbar kotun tarayya. Hoto: @YeleSowore
Source: Twitter

Kwace na’urorin IPOB da Radio Biafra

Kotun ta kuma ba da umarni cewa dukkan na’urorin watsa shirye-shirye, da duk kayan sadarwar IPOB da Radio Biafra su koma hannun gwamnatin tarayya nan take.

Wannan ya hada da duk wata na’urar da ake amfani da ita wajen watsa sakonnin IPOB a cikin gida ko daga waje.

A baya, lauyan gwamnatin tarayya, SAN Adegboyega Awomolo, ya roki kotu ta yanke wa Kanu hukuncin kisa, yana mai cewa dokar ta’addanci ta tanada hakan a matsayin tilas.

Sai dai Mai shari'a Omotosho ya ce duk da cewa laifuffukan Kanu sun cancanci hukuncin kisa, ya zabi nuna jin-kai, ya koma hukuncin daurin rai-da-rai.

Nnamdi Kanu ya birkita kotu a zaman karshe

Tun da fari, mun ruwaito cewa, an samu tashin hankali a babbar kotun tarayya a Abuja, bayan Nnamdi Kanu ya ki amincewa a karanta hukunci.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnati ta bukaci Alkali ya yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa

Mai shari'a James Omotosho ya dakatar da zaman kotun tare da umartar jami’an tsaro su fitar da Kanu daga dakin shari’ar don daidaita lamura.

Kotu ta yi watsi da bukatun da ya gabatar, ciki har da neman beli da kuma mika shari’ar zuwa kotun daukaka kara, inda Omotosho ya ce alkalami ya bushe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com