‘A Duba Tsufansa’: 'Dan Majalisa Ya Roki Alkali Ya Sassauta Hukuncin Nnamdi Kanu
- Ɗan majalisar tarayya ya roki alkalin kotun tarayya alfarma wajen yanke hukunci kan shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu
- Hon. Obi Aguocha ya roƙi a tausaya wa Nnamdi Kanu a kotun tarayya mai zama a Abuja, bayan an same shi da laifin ta’addanci
- Ya bayyana kansa a matsayin wakilin Kanu, yana roƙon alkali ya tausaya masa, tare da gode wa kotu kan damar da ta ba shi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ɗan majalisar wakilai, Obi Aguocha, ya roƙi alfarma ga jagoran haramatacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Dan majalisar ya roki alkalin kotun da ya yi sassauci yayin shari’arsa a kotun tarayya Abuja wanda aka yi a yau Alhamis 20 ga watan Nuwambar 2025.

Source: Twitter
'Dan majalisa ya rokawa Kanu alfarma a kotu
Rahoton Punch ya ce dan majalisar ya roki hakan ne jim kadan bayan hukuncin da aka yankewa Kanu kan zargin ta'addanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aguocha, wanda ke wakiltar Ikwuano/Umuahia North/Umuahia ta Kudu, ya yi jawabi ne bayan kotu ta same Kanu da laifuffuka bakwai na ta’addanci.
Ya ce:
“Na roƙi a yi masa rahama da sassauci, ina neman zaman lafiya da kwanciyar hankali ba a Kudu maso Gabas kaɗai ba, har da Najeriya.”
Aguocha ya ƙara da cewa yana nan kusan duk lokacin zaman kotu saboda shi ne wakilin Nnamdi Kanu na kai tsaye a majalisar tarayya.
Ya yi godiya ga kotu, yana roƙon alkali ya “tausaya da nuna adalci,” yana jaddada cewa zaman lafiya da mafita na buƙatar haɗin kai a Najeriya.

Source: Twitter
Tsawon lokaci da aka shafe ana shari'ar Kanu
Aguocha ya kuma roƙi masu gabatar da ƙara su duba faɗin yanayin matsalar tsaro a ƙasar, yana mai cewa akwai wasu mutane a wajen kotu “da suke aikata abin da ya fi haka muni” fiye da abin da ake zargin Kanu da shi.
Ya tunatar da kotu cewa shari’ar Kanu ta ɗauki kusan shekaru 10 tana gudana, sannan wanda ake tuhumar yanzu yana cikin shekaru 50 zuwa sama, wanda ya dade ba tare da iyalansa da al’ummarsa ba.
Ya ce:
“Ina roƙon ubangiji ya nuna rahama ya kuma sassauta hukunci da adalci. Ni abokin kotu ne, kuma ina gode muku da damar magana.”
Daga baya, Mai Shari’a Omotosho ya same Kanu da laifi a dukkan tuhumar ta’addanci bakwai da ake yi masa, cewar Channels TV.
Bayan haka, sai alkali ya dakatar da ci gaban zaman, ya umarci waɗanda ke son halartar yanke hukunci su dawo kotu minti 15 kafin ƙarfe 4:00 na yamma.
Bukatar gwamnati ga kotu kan bukacin Kanu
An ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta samu jagoran kungiyar 'yan aware ta Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu da laifi.
Alkalin kotun mai shari'a James Omotosho, ya samu Nnamdi Kanu da laifi a dukkkanin tuhume-tuhume bakwai da ake yi masa.
Bayan samun Kanu da laifi, gwamnatin tarayya ta hannun lauyanta ta bukaci kotun ta yanke masa hukuncin kisa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

