Yadda Gwamnati Ta Bukaci Alkali Ya Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Kisa
- Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta samu jagoran kungiyar 'yan aware ta Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu da laifi
- Alkalin kotun mai shari'a James Omotosho, ya samu Nnamdi Kanu da laifi a dukkkanin tuhume-tuhumen ta'addanci bakwai da ake yi masa
- Bayan samun 'dan tawaren mai shekaru 68 da laifi, gwamnatin tarayya ta hannun lauyanta ta bukaci kotun ta yanke masa hukuncin kisa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin kisa kan Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB da aka haramta.
Gwamnatin Najeriya ta bukaci hakan ne bayan kotu ta same shi da laifin ta’addanci a kan tuhume-tuhume bakwai da ake yi masa a ranar Alhamis.

Source: Twitter
Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa lauyan gwamnatin tarayya, Adegboyega Awomolo, ne ya bukaci hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkali ya samu Nnamdi Kanu da laifi
Allakin kotun, mai shari'a James Omotosho, yayin yanke hukuncinsa, ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da shari’arsu bisa shaidu masu gamsarwa.
Mai shari'a James Omotosho ya samu Nnamdi laifi kan dukkan tuhume-tuhume guda bakwai da gwamnatin tarayya ta shigar a kansa, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar da labarin.
Wace bukata gwamnati ta nema?
Bayan sanar da samun Kanu da laifi, jagoran lauyoyin gwamnatin tarayya, Adegboyega Awomolo, SAN, ya roki kotu da ta yanke hukuncin mafi tsanani da doka ta tanada a karkashin dokar hana ta'addanci ta 2013 da aka yi wa gyara.
Awomolo ya tunatar da kotu cewa dokar ta tanadi hukuncin kisa ga wasu daga cikin manyan laifuffukan da aka samu Nnamdi Kanu da su.
"Ya mai girma mai shari'a, bayan wannan hukuncin samun laifi, abin da ya rage kawai shi ne yanke hukunci bisa doka."
"Hukuncin da doka ta tanada kan tuhume-tuhume na 1, 2, 4, 5 da 6, a karƙashin sashe na 12H na dokar hana ta'addanci ta 2013, shi ne kisa."
“Da girmamawa, ina sanar da kotu cewa babu zabin wani hukunci. Hukuncin da za a iya yankewa kawai shi ne hukuncin kisa, domin doka ta ba ka wannan ikon, kuma muna sa ran kotu za ta yi hakan.”
- Adegboyega Awomolo
Sai dai Alkalin kotun tarayyan ya yi rangwame, ya yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin daurin rai da rai mai tsanani.
Gwamnatin tarayya ba ta samu yadda ta ke so ba, idan hukuncin ya zauna, Nnamdi Kanu zai kare rayuwarsa a gidan maza.

Source: Twitter
Karanta wasu labaran kan Nnamdi Kanu
- A karshe, kotu ta kama Nnamdi Kanu da laifin ta'addanci, ta yanke masa hukunci
- Nnamdi Kanu ya birkita kotu yayin da za a yanke masa hukunci kan ta'addanci
- Ba fashi: Alkali zai yankewa Nnamdi Kanu hukunci bayan fitar da shi daga harabar kotu
Kotu ta yankewa Nnamdi Kanu hukunci
A wani labarin kuma, kun ji cewa alkalin babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja, ta yanke hukunci ga jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu.
Alkalin kotun mai shari'a James Omotosho ya yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da laifi a zargin aikata ta'addanci.
Mai shari'a James Omotosho ya kuma yankewa Nnamdi Kanu hukuncin shekara 20 a gidan gyaran hali kan wani laifin da aka same shi da aikatawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


