Bayan Saukar Farashin Mai, Matatar Dangote Ta Faɗi dalilin Samun Sauki da Aka Yi

Bayan Saukar Farashin Mai, Matatar Dangote Ta Faɗi dalilin Samun Sauki da Aka Yi

  • Kamfanin Dangote ya yi magana game da rage farashin man fetur da yan kasuwa suka yi a kwanakin nan
  • Ya bayyana cewa raguwar farashin man fetur da ’yan kasuwa suka yi ya biyo bayan rangwamen da aka yi a watan Nuwambar 2025
  • Kamfanin ya ce ya rage farashin daga N877 zuwa N828 a matakin ganga, tare da saukar da farashin teku daga N854 zuwa N806.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Matatar man Dangote ta yi ƙarin haske game da samun saukin farashin man fetur da aka samu.

Kamfanin ya ce saukin da 'yan kasuwa suka samar sakamakon rage farashinsu ne a ranar 6 ga watan Nuwambar 2025.

Dangote ta yi ƙarin haske kan faduwar farashin fetur
Matatar Dangote da ke Kudancin Najeriya da shugaban kamfanin, Aliko Dangote. Hoto: Dangote Group.
Source: UGC

A cikin wata sanarwar da The Nation ta samu, kamfanin ya ce an samu ragin ne bayan saukar da farashi ba saboda janye harajin 15% na shigo da kaya ba.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Matasa 16 da suka gama digiri sun mutu a hanyar zuwa sansanin NYSC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musabbabin raguwar farashin mai da aka yi

Ya bayyana cewa sun saukar da farashin ga N877 zuwa N828 a matakin ganga, tare da rage farashin teku daga N854 zuwa N806.

Kamfanin ya ce yana da niyyar samar da ingantaccen mai kuma mai araha ga jama’a, domin tabbatar da mutane sun ci moriyar tacewa da ake yi a gida.

Dangote ya karyata rahotannin da ke cewa saukar farashin man fetur a gidajen mai ya faru ne sakamakon gwamnatin tarayya ta dakatar da harajin shigo da mai da dizal na kashi 15.

Ya bayyana irin waɗannan ikirari a matsayin marasa tushe, masu ruɗarwa, kuma ba su da dangantaka da gaskiyar abin da ke faruwa a kasuwa.

Dangote ya yi bayani cewa abin da ya haifar da saukar farashin mai shi ne raguwar da ya yi da 5.6% a ranar 6 ga Nuwamba, cewar Punch.

Kamfanin Dangote ya magantu kan saukar farashin mai
Shugaban kamfanin Dangote a Najeriya. Hoto: Dangote Foundation.
Source: Facebook

Matsayar Dangote game da shigo da mai

Kara karanta wannan

Saukar farashi: Yadda manoma ke tafka asara bayan girbi a daminar bana

Kamfanin ya ƙara bayyana cewa harajin shigo da 15% tuni ya sami amincewar shugaban ƙasa tun ranar 21 ga Oktobar 2025, kuma matsayinsa na aiwatarwa ba shi da tasiri ko kaɗan kan farashin da kamfanin ya fitar.

Dangote ya kuma soki ci gaba da shigo da kaya marasa inganci kuma masu tsada, yana mai bayyana hakan a matsayin abin da ke cutar da masana’antar cikin gida, kamar yadda ya faru da sashen masana'antar tufafi a baya.

Kamfanin ya jaddada aniyar samar da mai mai inganci da farashi mai gogayya da saura, tare da taka rawa wajen daidaita farashin kasuwa.

A ƙarshe, kamfanin ya bukaci masu ruwa da tsaki da kafafen yada labarai su dogara da bayanan da aka tabbatar, domin amfanin jama’ar Najeriya.

Za a daina shigo da mai daga waje

Mun ba ku labarin cewa matatar Dangote ta rage farashin man fetur da ₦49 a kan kowace lita, abin da ya girgiza kasuwar sayar da mai a Najeriya.

'Yan kasuwar mai sun ce wannan mataki zai iya kawo ƙarshen shigo da fetur daga waje, saboda farashin Dangote ya fi rahusa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun dawo, sun hana manoma taba amfanin gona sai da harajin miliyoyi

Amma wasu masana sun gargadi gwamnati cewa dakatar da shigo da mai gaba ɗaya zai iya haifar da karancin mai a kasuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.