Tsautsayi: Matasa 16 da Suka Gama Digiri Sun Mutu a Hanyar zuwa Sansanin NYSC
- Hatsarin mota ya rutsa da matasa da ke kan hanyar zuwa sansanin daukar horo na NYSC yayin da suke shirin fara bautar kasa
- Rahotanni sun nuna cewa matum 16 daga cikin 18 da motar bas ta dauko da nufin zuwa Gombe, sun riga mu gidan gaskiya
- Wannan lamari ya tada hankulan jama'a, tuni dai hukumar FRSC ta fara bincike domin gano abin da ya haddasa hatsarin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - An shiga tashin hankali yayin da wasu matasa da ke shirin fara aikin bautar kasa (PCMs) suka gamu da ajalinsu a hanyar zuwa sansanin NYSC na jihar Gombe.
Lamarin ya faru ne yayin da hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta fara shirin horar da yan rukunin C a fadin jihohin Najeriya.

Source: Twitter
Matasa 16 sun mutu a hanyar Gombe
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa matasan su 16, wadanda suka kammala digiri sun mutu ne a wani mummunan hatsari da ya rutsa da su a hanyar zuwa sansanin daukar horon NYSC a Gombe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalibai biyu kacal daga cikin 18 da ke cikin motar bas mai daukar fasinjoji 18 ne suka tsira daga hatsarin, amma su kansu an ce suna cikin mawuyacin hali a asibiti.
Rahotanni sun tabbatar da cewa dukkan waɗanda suka mutu ɗalibai ne da suka kammala karatu a Jami'ar Adeyemi Federal University of Education (AFUED), da ke jihar Ondo.
Yadda hatsarin ya faru a hanyar zuwa gombe
Matasan da ke shirin fara bautar ƙasar na tafiya ne a cikin wata bas mai kujeru 18 lokacin da hatsarin ya faru. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa:
"Hatsarin ya kasance mai muni sosai, mutane sun mutu yayin da wadanda suka tsira suka samu raunuka masu tsanani.”
Jami’an bada agajin gaggawa sun ciro gawarwakin wadanda suka mutu a hadarin, sannan suka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa.
Shin NYSC ta yi magana kan hatsarin?
Har zuwa lokacin da muka hada wannan rahoto, hukumar NYSC ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa watau FRSC na jagorantar bincike don gano musabbabin haɗarin, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Source: Twitter
Sai dai wannan ibtila'i da matasan suka gamu da shi ya sake tayar da muhawara musamman a kafafen sada zumunta game da lalacewar hanyoyi a kasar nan.
Wasu sun nemi a tilastawa direbobin motoci bin dokokin hanya da kaucewa gudun da ya wuce kima, sannan sun nemi NYSC ta duba tura matasa jihohi mafi kusa don gujewa wa doguwar tafiya.
Tirela ta murkushe mutane a Ondo
A wani rahoton, kun ji cewa an rasa rayuka da dama da wata tirela dauke da buhunan siminti ta sauka daga kan titi, ta fada kan mutane a jihar Ondo.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Kasa (FRSC) reshen Ondo, Samuel Ibitoye, ya tabbatar da cewa mutane takwas ne suka mutu, maza biyar, mata biyu fa yaro daya.
Ya ce motar ta murkushe katanga a gaban jami’ar kafin ta sauka daga hanya ta afka wa shagunan jama'a a gefen titi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


