Bayan Kashe Kiristoci a Coci, Ƴan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kwara, Sun Sace Mutane
- 'Yan bindiga sun kai sabon hari kayen Bokungi, karamar hukumar Edu ta jihar Kwara, inda suka sace manoma a cikin gona
- Wannan harin ya biyo bayan na garin Eruku a cikin kasa da awanni 24, lamarin da ya kara tsananta tsoro ga al'ummar Kwara
- Wani jami'in rundunar ƴan sanda ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa ana kokarin ceto mutanen da aka sace a Bokungi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Tashin hankali ya sake dawowa a jihar Kwara bayan da wasu ƴan bindiga suka kai hari a kauyen Bokungi da ke ƙarƙashin masarautar Lafiagi.
An rahoto cewa 'yan ta'addar sun yi garkuwa da manoma hudu a harin da suka kai masu lokacin suna aikin girbi a gonakin shinkafa da yammacin ranar Laraba.

Source: Original
'Yan bindiga sun kai sabon hari Kwara

Kara karanta wannan
Me ke faruwa? Fusatattun matasa sun rufe babban titi a Arewa, sun hana kowa wucewa
Sabon harin ya zo ne cikin sa’o’i 24 bayan 'yan ta'addan sun kai hari karamar hukumar Ekiti, inda suka kashe mutane, suka tafi da sauran masu ibada a coci, in ji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan bindigar sun mamaye garin a bazata, suka yi wa manoman kawanya yayin da suke tattara shinkafar da suka girbe.
Rahotanni sun ce ba a samu wani dauki daga jami’an tsaro ba, lamarin da ya ba ƴan bindigar damar iza keyar manoman zuwa cikin daji.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa harin ya faru ne tsakanin ƙarfe 6:30 zuwa 7:00 na yamma, lokacin da manoman suke cikin gonaki.
Mazauna Kwara sun shiga tashin hankali
Yayin da aka kai harin, mutanen garin Bokungi sun shaidawa jaridar This Day cewa yanzu hankulansu a tashe yake, inda kowa ke tsoron zuwa gona.
Wasu ma sun bayyana cewa hare-haren da ake yawan samu a yankin sun tilasta wasu iyalai barin kauyen gaba ɗaya.
Wani mazaunin yankin ya ce:
“Mun kasa samun kwanciyar hankali. Yanzu kowa yana tsoron zuwa gona, ka da ya je a kashe shi ko a sace shi. Lamarin nan ya wuce duk yadda ake tunani.”
Al'ummar yankin sun roki gwamnati ta tura karin jami’an tsaro saboda hare-hare sun yi yawa, musamman a lokacin da jama'a ke girbe amfanin gona.

Source: Twitter
‘Yan sanda sun yi martani kan sabon hari
Wani jami’in ƴan sanda a karamar hukumar Edu a tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an fara bincike tare da kokarin gano inda aka tafi da manoman.
Dan sandan da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa rundunar ta tura rahoto zuwa hedikwatar jihar don neman karin dakaru.
Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar ƴan sandan jihar da gwamnatin Kwara ba su fitar da sanarwa kan harin a hukumance ba.
Matsalar tsaro: An rufe makaratu a Kwara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kwara ta bada umarnin rufe dukkanin makarantu kananan hukumomi hudu saboda karuwar tsaro a jihar.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ba da umarnin a rufe dukkanin makarantu a kananan hukumomin Isin, Irepodun, Ifelodun da Ekiti.
Gwamnati ta ba da wannan umarnin rufe makarantun ne ta hannun kungiyar malamai ta NUT reshen jihar a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
