Gwamnatin Zamfara Za Ta Yi Wa Mutane 200 Auren Gata, an Ji Wadanda Za Su Amfana
- Gwamnatin jihar Zamfara ta hannun Hukumar zakka da wakafi na shirin gudanar da auren ga wata ga wasu marayu da suka rasa iyayensu
- Shugaban hukumar Zakka da wakafi ta Zamfara, Malam Habibu Balarabe, ya bayyana cewa an kammala shirye-shiryen aurar da marayu har 200
- Hakazalika, shugaban hukumar ya bayyana cewa za a gudanar da rabon jarin kasuwanci ga mata masu kananan sana'o'i domin tallafa musu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara, ta hannun hukumar zakka da wakafi, ta shirya gudanar da auren gata ga wasu marayu.
Gwamnatin ta Zamfara ta kammala shirye-shiryen ɗaukar nauyin aurar da marayu 200 a fadin jihar.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa shugaban Hukumar zakka da wakafi, Malam Habibu Balarabe, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar.
Yaushe za a yi auren gata a Zamfara?
Malam Habibu Balarabe ya ce an tsara gudanar da bikin auren a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, 2025, a harabar hukumar.
Ya tabbatar da cewa an tantance kuma an zaɓi dukkan marayun da za su amfana da shirin, rahoton ya zo a jaridar The Guardian.
“Hukumar ta riga ta tantance ta kuma zaɓi dukkan wadanda za su amfana da wannan taimako.”
- Malam Habibu Balarabe
Gwamnati za ta bada tallafi
Baya ga shirin aurar da marayu, hukumar za ta ba wa mata 200 da ke gudanar da kananan sana’o’i tallafin jari domin inganta rayuwarsu da faɗaɗa harkokin kasuwancinsu.
Malam Habibu Balarabe ya ce mata 100 sun kammala horo na makonni uku kan kiwon kaji, kuma za a ba su kayan fara sana’a domin su fara neman na abinci.
Ya kara da cewa hukumar ta kuma shirya biyan wasu basussuka da aka shigar da kara kansu a kotunan Shari’a da kuma cibiyoyin gyaran hali a fadin jihar.
Shugaban hukumar ya kara bayyana cewa wasu marayu sun kammala horo kan samun ilimin kwamfuta, kuma za a ba su kayan fara amfani da kwamfuta a yayin bikin.

Source: Original
Wani mazaunin Zamfara, Jamil Abdullahi, ya shaidawa Legit Hausa cewa shirin aurar da marayun abin a yaba ne.
"Gaskiya wannan abin a yaba ne domin zai taimaka sosai ga marayun da ke bukatar aure amma masu rike da su ba su da halin aurar da su."
"Kuma wannan jarin da za a ba mata masu kananan sana'o'i zai taimaka musu wajen bunkasa kasuwancinsu."
- Jamil Abdullahi
Karanta wasu karin labaran kan jihar Zamfara
- An kai karar Gwamna Dauda wurin Trump, an bukaci ya kakaba masa takunkumi
- Babbar magana: Kotu ta kwace kujerar dan Majalisar Tarayya daga Jihar Zamfara
- Gwamna Dauda Lawal ya tara malaman Musulunci a Zamfara, ya nemi alfarmarsu
Ma'aurata sun roki shiga auren gata
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta sanar da shirin gudanar da auren gata ga mutane 2,000 da suka hada da mata da maza.
Wasu mazan aure a jihar sun roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya ba su damar shiga shirin domin su ƙara aure kamar yadda addini ya halatta.
Magidanta da ke zama da mace ɗaya sun ce wannan dama ce gare su don su kara aure ba tare da wahalar kuɗin lefe da kayan ɗaki ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


