Tinubu Ya Taya Jonathan Murnar Cika Shekaru 68, Ya Fadi Kyawawan Halayensa

Tinubu Ya Taya Jonathan Murnar Cika Shekaru 68, Ya Fadi Kyawawan Halayensa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan murnar cikar sa shekaru 68 da haihuwa
  • Shugaba Tinubu ya yaba da yadda Jonathan ya nuna jajircewar kishin ƙasa a 2015, wanda ya ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya
  • Ya kuma yi addu’ar samun lafiya mai inganci ga Jonathan da iyalinsa, tare da bayyana tasirin kwarewar Jonathan a nahiyar Afrika

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, murnar cika shekaru 68 da haihuwa.

Wannan na kunshe a cikin sakon taya murnar da Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 20 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Ran maza ya baci: Tinubu ya umarci sojoji su ruguza 'yan ta'adda a Najeriya

Shugaban kasa ya taya Tinubu murnar zagoy
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: Goodluck Jonathan/Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Sanarwar, wacce hadimin shugaban kasa Dada Olusegun ya wallafa a shafin X ta bayyana gamsuwa da rawar da Jonathan ya taka wajen gina ƙasa da ƙarfafa dimokuraɗiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya taya Jonathan murnar cika shekaru 68

Shugaba Tinubu ya ce wannan rana ta zagayowar haihuwar Jonathan ta zama dama ta tunawa da irin gudunmawar da tsohon Shugaban ya bayar a tarihin siyasar Najeriya.

Ya jinjina da yadda Jonathan ya taka rawar gani musamman yadda ya karɓi sakamakon zaɓen 2015 cikin natsuwa da nuna kishin ƙasa, wanda ya daukaka Najeriya a idon duniya.

Tinubu ya ce Jonathan ya fito da Najeriya a idon duniya
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan
Source: Getty Images

A cikin sakon nasa, Shugaba Tinubu ya tuna ganawa da ya yi da Jonathan a lokacin da yake kan mulki da ma bayan nan.

Ya bayyana cewa waɗannan tattaunawa sun taimaka wajen samun daidaituwa da ci gaban ƙasa a wasu muhimman lokuta.

Shugaban ya ce goyon bayan da Jonathan ya samu a 2010 da kuma nasararsa a zaɓen 2011 sun nuna yadda ya samu amincewar al’umma a lokacin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi sauyi a gwamnati, ya ba ɗanuwan marigayi Shehu Shagari muƙami

Shugaba Tinubu ya jinjinawa Jonathan

Tinubu ya kuma bayyana cewa jajircewar Jonathan wajen aikin diflomasiyya a matakin ƙasa da ƙasa, musamman a Afrika, ta sanya shi zama shugaba mai tasiri.

Ya ce 'yan nahiyar nan suna ganin kokarinsa wajen bunƙasa dimokuraɗiyya, zaman lafiya da ‘yanci a tsakanin kasashen Afrika.

Shugaban ya ce kokarin Jonathan na jagorantar kwamitoci ya sanya shi a cikin sahun shugabanni masu biyayya ga doka, kuma yana ƙara bai wa Najeriya daraja ta musamman.

Shugaban ya yi addu’ar Allah ya ƙara ba Jonathan lafiya da ƙarfin jiki, tare da sanya albarka a iyalinsa, musamman matarsa Dame Patience Jonathan.

Tinubu: An matsawa Jonathan ya hakura da takara

A baya, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, na fuskantar matsin lamba daga manyan ’yan siyasa da dattawan yankin Neja Delta kan batun zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan yankin na ƙoƙarin ganin cewa Jonathan bai tsaya takara ba a babban zaɓen 2027, domin su a cewarsu, rashin takarar zai taimaki yankin.

Kara karanta wannan

Abu ya kacame, sabon shugaban PDP da tsagin Wike na iya arangama a taro

A maimakon ya tsaya takara, rahoton ya ce waɗannan shugabanni sun fi son Jonathan ya mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya samu damar neman wa’adin mulki na biyu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng