Nnamdi Kanu Ya Birkita Kotu yayin da za a Yanke Masa Hukunci kan Ta'addanci

Nnamdi Kanu Ya Birkita Kotu yayin da za a Yanke Masa Hukunci kan Ta'addanci

  • An samu tashin hankali a babbar kotun tarayya a Abuja, bayan Nnamdi Kanu ya ki amincewa a karanta hukunci
  • Alkali James Omotosho ya dakatar da zaman kotun tare da umartar jami’an tsaro su fitar da Kanu daga dakin shari’ar
  • Kotu ta yi watsi da bukatun da Kanu ya gabatar, ciki har da neman beli da kuma mika shari’ar zuwa kotun daukaka kara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An samu yamutsi a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda zaman shari’ar Nnamdi Kanu ya rikide zuwa wani yanayi na hayaniya.

Kanu ya dage cewa ba za a iya karanta hukuncin ba illa sai idan kotu ta nuna masa dokar da ta haramtawa wanda ake tuhuma damar gabatar da rubutaccen jawabi.

Kara karanta wannan

A karshe, kotu ta kama Nnamdi Kanu da laifin ta'addanci, ta yanke masa hukunci

Dan ta'addan IPOB, Kanu a kotu
Nnamdi Kanu a kotun tarayya. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Getty Images

Rahoton Vanguard ya bayyana cewa ana tsare da Nnamdi Kanu ne saboda tuhume-tuhumen ta’addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rashin jituwa tsakanin Kanu da kotu ya jawo tsaikon shari’a yayin da mai shari’a, James Omotosho, ya dakatar da zaman don bai wa jami’an tsaro damar fitar da shi daga dakin kotu.

Kotun ta yi watsi da bukatun Nnamdi Kanu

Mai shari'a Omotosho, yayin karanta hukuncin kan bukatun da Kanu ya shigar, ya bayyana cewa sababbin bukatun sun ƙunshi batutuwan da Kanu ya taɓa gabatarwa a baya.

Don haka kotun ta ce babu wani sabon abu da zai sa a sake bude wata sabuwar hanya ta shari’a a gaban kotu.

Kotu ta nuna cewa sashen doka na 306 na ACJA 2015 ya haramta dakatar da shari’a a kan wani laifi, don haka ba za a iya dakatar da zaman ba, balle a mayar da shi zuwa kotun daukaka kara.

Nnamdi Kanu yayin zaman Kotu
Shugaban 'yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Twitter

Kotun ta ce za ta yi la’akari da wasu daga cikin batutuwan da Kanu ya gabatar yayin karanta hukunci, amma ta yi watsi da batun beli, tana cewa an riga an shiga matakin karshe na shari’ar.

Kara karanta wannan

Ba fashi: Alkali zai yankewa Nnamdi Kanu hukunci bayan fitar da shi daga harabar kotu

Kanu ya birkita zaman kotu a Abuja

Yayin da alkali ya koma gaban kotu domin fara karanta hukunci, Nnamdi Kanu ya tsaya tsayin daka yana cewa kotu ba ta da hurumin cigaba da karanta hukuncin.

The Cable ta rahoto cewa ya fara kururuwa yana cewa:

“Ka nuna min dokar! Ina dokar?”

Wannan ya sa aka tilasta dakatar da karanta hukuncin, yayin da wata hayaniya ta tashi a kotu babu shiri.

A cikin zafafan kalamansa, ya zargi alkali da nuna son kai yana faɗin:

“Kai ba ka san doka ba, kana nuna son kai.”

Jami’an tsaro da ke cikin kotu sun yi kokarin fitar da shi, amma ya ci gaba da yi musu ihu yana cewa:

“Kada ku taba ni! Kada ku taba ni!”

An yankewa 'yan ta'adda hukunci a kotu

A wani labarin, kun ji cewa wata kotun tarayya a Abuja ta yanke wa wani dan ta'addan ISWAP hukunci.

Kara karanta wannan

Kiraye kiraye sun yawaita, ana son Tinubu ya yi murabus daga shugabancin Najeriya

An yankewa dan ta'addan hukuncin shekara 20 ne bayan samunsa da laifuffukan ta'addanci a Najeriya.

Hukuncin ya zo daidai da lokacin da 'yan ta'adda ke cigaba da kai zafafan hare-hare Najeriya suna sace mutane.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng