Saukar Farashi: Yadda Manoma ke Tafka Asara bayan Girbi a Daminar Bana

Saukar Farashi: Yadda Manoma ke Tafka Asara bayan Girbi a Daminar Bana

  • Manoma a Taraba na fuskantar asara sakamakon mummunan faɗuwar farashin amfanin gona musamman masara da shinkafa
  • Wasu manoma sun bayyana cewa sun kashe miliyoyin Nairori a shuka da girbi amma farashin kasuwa ya yi kasa sosai a bana
  • A cewar manoma da dama, shigo da hatsi daga ƙasashen waje da rashin tallafin gwamnati na yin barazana ga shuka kayan noma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - A jihar Taraba, daruruwan manoma sun shiga wani hali na damuwa bayan fuskantar mummunan faɗuwar farashin masara da shinkafa.

Lamarin da ya sa da dama daga cikinsu suka kasa dawo rabin abin da suka kashe a damunarr bana.

Wasu manoma a gona
Wasu manoma na aiki a gona. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa matsalar ta sa wasu manoman sun ce ba za su iya komawa noman rani ba saboda ƙarancin kuɗin aiki gonakinsu.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta fadi halin kunci da ta shiga bayan sace dalibai mata a Kebbi

Farashin kayan noma ya yi kasa

Rahotanni daga kasuwannin jihar Taraba sun nuna cewa farashin buhun masara da shinkafa ya faɗi sosai, inda buhu mai nauyin kilo 100 ke tsakanin N20,000 zuwa N28,000 kacal.

Farashi ya yi ƙasa da tsammanin manoma musamman ganin yadda farashin taki da aikin noma ya haura a kakar bana.

Manoman sun bayyana cewa hatsin da suke samu yanzu yana zama musu asara, musamman saboda hauhawar farashin kayan masarufi.

Labarin manoman da suka yi asara

Wani manomi daga Jalingo, Yau Aliyu ya ce ya kashe N1,400,000 daga shuka zuwa girbi a gonar masara amma ya samu buhuna 30 kacal.

Manomin ya bayyana cewa idan ya sayar da su a kan N20,000 kowanne, zai samu N600,000 ne kawai, wannan zai sa ya yi asarar N800,000.

Wata kasuwa da ake sayar da kayan abinci
Wasu kayan abinci da farashinsu ya yi kasa a kasuwa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Saboda asarar da ya yi, ya ce hakan ya hana shi komawa noman rani saboda babu kuɗin da zai yi amfani da su.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun dawo, sun hana manoma taba amfanin gona sai da harajin miliyoyi

Shi ma Nuhu Dauda daga Mutum Biyu a Gassol ya ce noman waken suya ne ya cece shi, domin bai samu komai ba a noman masara da shinkafa.

Wani manomi ya fadi dalilin yin asara

Wani manomi a Taraba, Lawal Suleiman, ya ce farashin kayayyakin girbi ya zama masifa ga manoma.

Ya bayyana cewa buhun masara da shinkafa ya yi ƙasa matuƙa, manoma sun yi asarar fiye da rabin abin da suka kashe.

Suleiman ya zargi gwamnatin tarayya da shigo da masara da shinkafa daga ƙasashen waje, abin da ya karya farashin kayayyakin cikin gida.

Legit ta tattauna da manoma a Gombe

A Gombe, wani manomi daga Yamaltu Deba ya koka da rikicin makiyaya da ya ce ya shafe shekaru 30 yana addabar su.

A tattaunawa da Legit Hausa, Ibrahim Aliyu ya ce:

"Ana ta fama da matsalar makiyaya, amma duk laifin gwamnati ne. Ba yadda za a yi a ce an gagara magance matsalar makiyaya a sama da shekara 30."

Wani manomi da ya yi noma a karamar hukumar Dukku, Usman Muhammad, ya ce farashin amfanin gona bai yi daidaita da abin da suka kashe a gona ba.

Kara karanta wannan

An kashe shanu kusan 300 a mummunan hari kan makiyaya a Benue

Usman ya bayyana wa Legit Hausa cewa:

'Wanda bai yi noma ba a bana ya fi cin riba. Ni ma akwai alamun wata shekara kayan abinci zan saya maimakon kashe kudin a gona."

An yi rikicin manoma/makiyaya a Gombe

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe ta dauki mataki bayan rikicin manoma da makiyaya a yankin Funakaye.

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya yi kamari kuma ya jawo asarar rayuka tare da jikkata wasu mutane.

A wani mataki na magance matsalar, gwamnatin Gombe ta dakatar da sarakuna biyu a yankin saboda gazawarsu wajen dakile rikicin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng