Gwamnan Binuwai Ya Watsar da Kalaman Trump, Ya Karyata Kisan Kiristoci a Jiharsa

Gwamnan Binuwai Ya Watsar da Kalaman Trump, Ya Karyata Kisan Kiristoci a Jiharsa

  • Gwamnan jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya fito da bayanai a kan zargin cewa ana ware kiristoci, ana kashe su saboda addininsu a Najeriya
  • Ya bayyana cewa rikice-rikicen da ake fama da su ba su kai matsayin da za a kira shi kisan kare dangi ba ba, kuma ya karyata batun jihadi a Najeriya
  • Alia ya ce ya yi bayani kai tsaye ga jakadan Amurka domin kore rahotannin da ba su da tushe na cewa Najeriya kasa ce da ke kashe kiristoci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Benue – Gwamnan jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya bayyana cewa babu abu mai kama da kisan kiyashi na addini ko kabila ko na kowanne rukuni a fadin jihar.

Kara karanta wannan

"Su nemi taimako": Amaechi ya ga gazawar gwamnati wajen yaki da ta'addanci

Ya yi takaicin yadda batun ya samo asali daga wasu jami’an gwamnatin Amurka da ke cewa kasar nan da cewa ana kisan kiristoci.

Gwamnan Binuwai ya karyata kisan kiristoci a Najeriya
Gwamnan jihar Binuwai Hyacinth Alia Hoto: Fr. Hyacinth Lormem Alia
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa gwamnan na wannan batu ne yayin da ake sanya jiharsa a cikin daya daga cikin inda ake ganin ana kashe kiristoci.

Gwamnan Binuwai ya magantu kan tsaro

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa gwamnan jihar Binuwai ya karyata cewa babu wani abu mai kama da jihadi a sassan kasar nan.

A cewarsa:

“A jihata ta Binuwai, babu wani kisan kiyashi na addini, na kabila, na yanki ko na kasa. Abin da muke da shi shi ne matsalolin tsaro, amma ba zai taba kai matsayin kisan kare dangi ba. Duk mai shakku ya koma ya duba ma’anar kisan kiyashi na Majalisar Dinkin Duniya.”

Gwamnan, wanda babban fasto ne, ya yi wannan jawabi ne a taron tattaunawa kan kare hakkokin mutanen da suka rasa matsugunni da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta NHRC ta shirya a Abuja.

Gwamnan Binuwai ya karyata jihadi a Najeriya
Gwamna Hyacinth Alia na jihar Binuwai Hoto: Fr. Hyacinth Lormem Alia
Source: Facebook

Gwamnan ya kara da cewa ba a ko ina a Najeriya ake batun jihadi ba, kuma ko a jihohin Arewa maso Gabas da ISWAP da Boko Haram ke wannan ikirari, suna yi ne bisa kuskure.

Kara karanta wannan

Naira tiriliyan 1.4 sun yi ƙafa a CBN, an taso gwamnan babban banki ya yi bayani

Ya ce:

“A matsayina na babban limamin coci kuma gwamna, babu wani jihadi a Najeriya. Da akwai, ni ne mutum na farko da zan fito na kwarmata."

Gwamnan Binuwai ya gana da jakadan Amurka

A kan batun dangantakarsa da Amurka, gwamnan ya bayyana cewa ya kai ziyara ofishin jakadancin kasar domin fayyace yadda matsalar tsaro take a zahiri.

Ya ce wannan tattaunawa ta tabbatar da cewa rahotannin kisan kiyashi ba su yi daidai da ma’anar da Majalisar Dinkin Duniya ta samar ba.

Tun daga 2009, jihar Binuwai ke fama da hare-hare da kashe-kashe, inda kididdigar kungiyar ACLED ta nuna cewa sama da mutum 800 aka kashe.

Gwamnati ta zargi Trump da rura ta'addanci

A baya, mun wallafa cewa Sakataren gwamnati, George Akume ya ce Shugaban Amurka, Donald Trump, na cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya na kara baiwa kungiyoyin ‘yan ta’adda kwarin gwiwa.

George Akume ya tunatar da cewa kafin Trump ya zargi Najeriya da kisan gilla ga Kiristoci, tasirin ‘yan ta’adda na raguwa sosai, amma tun bayan kalamansa abubuwa suka lalace.

Kara karanta wannan

'Mutane da yawa sun mutu,' Tinubu ya dauki muhimmin alkawari ga al'ummar Filato

Sakataren gwamnati ya kara da cewa ya musanta zargin cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya, yana mai cewa bincike ya nuna cewa ‘yan ta’adda na kai hari ga coci da masallatai baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng