Ran Maza Ya Baci: Tinubu Ya Umarci Sojoji Su Ruguza 'Yan Ta'adda a Najeriya
- Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce shugaba Bola Tinubu ya ɗauki sababbin matakan tsaro bayan hare-hare a jihohi
- Mohammed Idris ya ce an umarci dakarun tsaro su gaggauta kawar da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da jama’a baki daya
- Shugaban ƙasa ya fasa tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje, ciki har da taron G20, domin mayar da hankali kan tsaron cikin gida
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja — Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci daukar mataki mai girma wajen yaki da 'yan ta'adda.
Shugaban ya bukaci haka ne bayan hare-haren da suka auku a jihohin Borno, Kebbi da Kwara da suka dauki hankali.

Source: Twitter
Wannan sanarwa ta fito ne a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba kamar yadda ma'aikatar yada labarai ta wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mohammed Idris ya ce shugaban ƙasa ya jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe, aka yi garkuwa da su ko kuma suka gamu da wani nau’in ta’addanci a makonnin da suka gabata.
Bola Tinubu ya dage tafiya saboda tsaro
Mohammed Idris ya ce kisan babban janar na sojoji a Borno, sace ɗalibai mata a Kebbi da kuma harin da aka kai coci a Kwara tunatarwa ne kan matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Ministan ya ce waɗannan abubuwan sun ƙara ƙaimin gwamnati wajen ganin an murƙushe ta’addanci da garkuwa da mutane baki ɗaya.
Ya ce domin mayar da hankali gaba ɗaya kan tsaron ƙasa, shugaba Tinubu ya fasa zuwa dukkan tarukan ƙasashen waje da ya shirya halarta, ciki har da taron G20 a Afirka ta Kudu.
An kara jami’an tsaro a wasu yankuna
A cewar ministan, shugaban ƙasa ya rattaba hannu kan ƙarin tura dakarun soja da ‘yan sanda zuwa yankin Eruku da wasu sassan jihar Kwara.
Wannan mataki, in ji shi, zai ƙarfafa kariya ga al’umma da kuma gaggauta mayar da martani idan an samu wani hari.

Source: Twitter
Ya kara da cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya je Kebbi a madadin Tinubu, inda ya gana da gwamna, shugabannin tsaro, sarakunan gargajiya da iyalan waɗanda aka sace.
Umarnin kakkabe ‘yan ta’adda a Najeriya
Ministan ya ce shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su “tarwatsa da rusa” duk wata hanyar sadarwa ta ‘yan ta’adda a fadin ƙasa.
A cewarsa, gwamnatin tarayya ba za ta lamunci wata hanyar da za ta ba wa miyagun mutane damar kai hari ba, musamman a yankunan makarantu da wuraren ibada.
Ya ce wannan mataki na nuna cewa gwamnati na kan turbar tabbatar da tsaro, kuma ba za ta kauce wa wannan aiki ba duk da ƙalubalen da ake fuskanta.
Mohammed Idris ya yi watsi da duk wani yunkuri da ake yi na juya matsalar tsaro zuwa rikicin addini.
Za a dauki sojoji 24,000 a Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar sojojin kasan Najeriya ta fadi shirin daukar karin dakaru.
Shugaban rundunar, Laftanar Janar Waidi Shuaibu ne ya bayyana haka yayin ziyarar da ya kai jihar Kaduna.
Ya bayyana matakan da rundunar za ta bi wajen daukar dakaru 24,000 domin kara yawan jami'ai su yaki 'yan ta'adda.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


